Wasu al'amura masu ban mamaki da rikitar wa a kan marigayi Mamman Shata

Wasu al'amura masu ban mamaki da rikitar wa a kan marigayi Mamman Shata

An haifa Mamman Shata a shekarar 1923 a karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina. Ya rasu a ranar 18 ga watan Yuni na 1999. Shata sanannen mawaki ne kuma ya rera wakoki masu tarin yawa. Kidan wakarsa shine kalangu. Ya yi waka ga hausawa da wasu sassa na Afirka, har da wadanda ba hausawa ba a sassan kasar nan.

Sunan mahaifiyarsa Lariya. Ta fito ne daga tsatson Fulani da ake kira da Fulata-Borno. Fulani ne da suka yi hijara daga masarautar Borno bayan jihadin Fulani na 1804, kuma suka samu matsuguni a kasar hausawa.

Ta hadu da mahaifin Shata mai suna Ibrahim Yaro, a lokacin da taje ziyarar 'yan uwanta. Daga baya kuwa suka yi aure har da yara uku. Yaro, Mamman Shata da 'yar uwarsa mai suna Yalwa sunan yaran.

Ga kadan daga cikin wasu abubuwan mamaki game da Shata:

Shata ya samo sunan Shata ne daga wani mutum mai suna Baba Salamu, dan uwansu ne.

Shata yaro ne da ya tashi da son neman na kansa. Ya fara siyar da goro tun yana karami, amma yana raba ribar ga mutanen da ya hadu dasu a kan hanyarsa ta komawa gida. Sau da yawa yana komawa gida hannu ba komai. Idan aka tambayesa yadda yayi da kudin sai yace, "Nayi shata da su". Ma'anar hakan kuwa itace yayi kyauta dasu.

Hakan kuwa yasa Baba Salamu ya ke kiransa da 'Mai-Shata', ma'anarsa kuwa mai kyauta.

Shata ya taba zuwa Hajji sau daya ne a rayuwarsa.

Duk da ya ziyarci kasashe masu yawa a rayuwarsa wadanda suka hada da Landan, Faransa da Amurka, Shata yayi aikin Hajji ne sau daya a rayuwarsa. An gano cewa wani Haru-Dan-Kasim ne ya biya masa a 1954; sanannen dan kasuwa ne a jihar Kano.

Shata dan siyasa ne kuma ya rike mukamai na siyasa kala-kala.

Shata ya taka rawar gani a siyasa a cikin rayuwarsa. Duk da siyasarsa ta adawa ce, ta kuwa masu sarauta da 'yan kasuwa duk ta biyayyace.

A 1970 ne ya lashe kujerar kansila a karamar hukumar Kankia a jihar Kaduna. A shekarun 1980 kuwa yana jam'iyyar GNPP ne kafin daga baya ya koma jam'iyyar NPN mai mulki.

A jamhuriya ta uku ne aka zabi Shata a matsayin shugaban karamar hukumar Funtua a karkashin jam'iyyar SDP. An tsigesa ne sakamakon halayyarsa ta adawa inda aka maye gurbinsa da Manjo Janar Shehu Musa Yar'adua mai ritaya.

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da shugaba Buhari ya ziyarta a 2019

Hazakarsa ta waka ta fara bayyana ne tun yana da yarinta.

Shata ya fara waka ne da sauran matasa a kauye don nishadi a dandali, bayan an ci abincin dare. Daga nan ne hazakarsa ta fara bayyana cikin sa'o'insa. Duk da yana hakan ne ba don kudi ba, kawai yana yi ne don nishadi.

Mahaifin Shata bai so dan sa ya zama mawaki ba.

Ibrahim Yaro bai so dan sa ya zama mawaki ba saboda al'adar wancan lokacin da ake kallon waka da roko. A matsayin mahaifinsa na bafulatani, ya so dansa ya zama manomi ne ko dan kasuwa ko kuma yayi sana'ar da zai alfahari da ita. Jajircewar Shata na cikar burinsa a wancan lokacin yasa ake kallontaa a matsayin rashin biyayya.

Shata ya dau shekaru 30 a matsayin tauraro, wakokinsa sun fi na kowanne mawakin hausa kasuwa a duniya.

A 1952 ne ya fara suna a Kano a lokacin da yayi wakar biki mai suna Bikin 'yan Sarki. A lokacin an aurar da sanannun yarimomi har 12 a Kano. Shata yayi shekaru 60 a masana'antar waka. A don haka ne ma ya zaman bai san yawan wakokinsa ba a duniya. Da yawa daga cikin wakokinsa da yayi na yarinta ba a yi musu faifai ba.

Shata na wakoki masu matukar ma'ana.

Shata ya wake kusan kowanne abu a kasar hausa. Ya wake noma da kiwo, al'ada, addini, tattalin arziki, siyasa, rundunar soji, dabi'a ta gari, nagarta, dabbobi, siye da siyarwa da sauransu.

Shata ya samu kambun girmamawa a gida da kasashen ketare, har da digirin giramamaw.

Shata ya samu lambobin yabon daga gwamnatin tarayya, kungiyoyi daban-daban, gwamnatin jihar Kano, ofishin jakadancin Najeriya, jami'ar California, Los Angeles da kuma digirin digirgir na girmamawa daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Hakan ya biyo bayan gudummawar da yake badawa ga cigaban kasar baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel