Tarihi da rayuwar Dakta Alhaji Mamman Shata
Legit.ng ta waiwaya muku tarihi da rayuwar Dakta Alhaji Mamman Shata Funtuwa, mawaki da a zamaninsa babu wanda yayi salon waka irin tasa, ya rayu a Kano da Katsina, kuma haifafen garin Huntuwa ne.
An haifi shahararren mawakin Hausa Marigayi Mamman Shata a garin Musawa ta jihar Katsina a shekarar 1923.
A daya daga cikin tattaunawar da aka taba yi da Mamman Shata ya ce ya fara waka ne tun daga kiriniyar yara ta rera waka kuma daga baya ta zamar masa sana'a.
Masana da yawa sunyi nazari da bincike a akan wakokin Shata amma har yanzu ba'a san takamaiman adadin wakokin da ya rera ba saboda dumbin yawansu.
Bincike ya tabbatar da cewar mahaifiyar Shata, Lariya, bafulatanar jihar Borno ce da aka haifa a garin Tofa dake jihar Kano inda iyayenta suka yi hijira bayan jihadin Usman Danfodio.
Larai ta auri mahaifin Shata, Ibrahim Yaro, wanda shi ma bafulani, ne a garin Tofa bayan mutuwar aurenta na farko. Bayan aurensu sun yi kaura ya zuwa wani jeji a jihar Katsina dake daf da garin Musa, inda daga bisani ya koma Musawa. Tarihi ya tabbatar da cewar dangin Shata ne suka kafa garin da yanzu jama'a suka fi sani da Musawa.
DUBA WANNAN: Siyasar Najeriya, Adawa na da amfani ga talakka
Mahaifiyar Shata su biyu ta haifa tare da mahaifinsa; Mamman Shata, da 'yar uwarsa, Yelwa, amma ta haihu a aurenta na farko.
Shata ya shafe mafi yawan shekarun rayuwarsa a garin Kano duk da dai yana da gidaje a Katsina, Kaduna, Kano, da ragowar wasu biranen Najeriya.
Mamman Shata ya rasu a shekarar 1999 kuma an binne shi a garin Daura kamar yadda ya bar wasiyya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng