Abubuwa takwas da ba lallai kunsan Alhaji Dakta Mamman Shata da su ba

Abubuwa takwas da ba lallai kunsan Alhaji Dakta Mamman Shata da su ba

Mamman Shata, an hafeshi ne a shekarar 1923 a Musawa local government ta jihar Katsina, ya Mutu a ranar 18 ga watan Yunin 1999. Shata, wani mawallafin hausa ne, yafi kowa yawan wakoki da aka rubuta.

Abubuwa takwas da ba lallai kunsan Alhaji Dakta Mamman Shata da su ba
Abubuwa takwas da ba lallai kunsan Alhaji Dakta Mamman Shata da su ba

1. Yayi aiki da hausawan Nijeriya da wasu sassa na Afrika dama wadanda ba Hausawa ba har kusan rabin karni.

2. Mahaifiyar mamman Shata, Lariya, ‘yar kabilar Fulani ce wadan da ake kira Fulata-Borno, Fulanin da suka yi hijira daga Borno bayan Fulani Jihad na shekarar 1804 suka kuma zauna a wasu sassan na Hausa.

3. Ta hadu da mahaifin Shata, Ibrahim Yaro, lokacin da ta je ziyarar dangi. Daga bisani, sunyi aure sun haifi yara uku Yaro, da Mamman Shata, da Yalwa.

4. Shata ya samu lakanin suna ne daga wani mutun da ake kira Baba Salamu, cikin 'yan uwansa. Shata da yana matashi yana sana’ar saida goro wanda bayan ya sayar ribar da ya samu sai raba ma mutanen kasuwa ko duk wanda ya hadu dashi a hanya ya dawo gida ba ko sisi.

Idan an tambayeshi abunda yayi da kudin sai yace nayi Shata da su, ma’ana yayi kyauta da su. Sakamakon haka baba Salamu sai yake kiran sa da ‘Mai Shata’, ma’ana mai kyautar da abun da ya samu.

5. Shata yaje Hajji so daya a rayuwar sa duk da dai ya ziyar ci kasashe da dama kamar su Ingila, Faransa, da Amuruka, Shata so daya ya taba zuwa hajji a rayuwarsa. Ance wani Shaharraren mai kudi ne kano ya biya masa a shekara ta 1954.

6. Shata ya kasance dan siyasa, wanda a shekara ta 1970 ya ci takara, in da ya zama kansila a karkashin Kankia local government, Kaduna State bayan nan kuma ya zama Chiyaman a Funtua local government.

DUBA WANNAN: Za'a kashe biliyan 15 a Aso Rock a 2018

7. Shata ya fara waka ne tare da samari a dandalin kauye. Har ya zama yafi kowa iya waka ba wai dan ya dauke ta sana’a ba. Duk da dai Mahaifinsa bad an yaso dan nasa ya zama mawaki ba saboda an dauke shi Roko.

8. A matsayin san a ba fillace maihaifin nasa ya so ace ya zama dan kasuwa ko manomi. Wanda bayan Shekara 30 da yayi yana waka ya zama zakara inda yafi kowa wakokin da ake so a cikin mawakan Hausa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng