Dauda Rarara ya ce daga yanzu sai Masoyan Buhari sun biya kudi zai yi masa waka

Dauda Rarara ya ce daga yanzu sai Masoyan Buhari sun biya kudi zai yi masa waka

- Dauda Kahutu Rarara ya ce sai Masoya sun biya kudi zai yi wa Buhari waka

- Babban Mawakin ya ce har gobe ya na tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari

- Rarara ya ce bai sauka daga jirgin Buhari ba, domin shugaban bai canza hali ba

Babban mawakin siyasa, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa ba zai sake yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari waka ba har sai an biya shi kudi.

Wannan karo mawakin ya ce dole kudin rera wakar ta fito daga hannun masoyan shugaban Najeriyar, ba wai ministan yada labarai ko wani ‘dan siyasar APC ba.

Dauda Kahutu Rarara ya shaidawa Duniya wannan ne a lokacin da ya zanta da gidan jaridar RFI Hausa.

Hakan na zuwa ne bayan mutane sun fara fitowa su na surutu, har ta kai wasu su na da-na-sanin zaben Muhammadu Buhari, a dalilin halin matsin lambar da aka shiga.

KU KARANTA: Atiku ya soki Shugaba Buhari, ya ce kamata ya yi fetur ya kara araha

A cewar Dauda Kahutu Rarara, duk masu sukar gwamnatin Buhari, ‘yan adawa ne wadanda tun farko ba su zabi jam’iyyarsa ta APC mai mulki a Najeriya tun 2015 ba.

Mawakin ‘yan siyasar ya ke cewa kamar barawo ne, idan aka buge shi, dole ya yi kuka.

Game da waka kuwa, Rarara ya ce ya na da abin fada da ya tanada, amma ba zai rera waka ba, muddin masoyan Buhari na ainihi ba su yi taron-dangi sun hada masa kudi ba.

Rarara ya bukaci masoyan shugaban kasar na hakika su yi karo-karon N1,000, shi kuma ya ce idan an yi hakan, zai fito da sabuwar waka domin bayyana kokarin APC.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon Sarkin Kano Bayero wajen taron Sarakunan Arewa

Dauda Rarara ya ce daga yanzu sai Masoyan Buhari sun biya kudi zai yi masa waka
Rarara ya ce Buhari bai saki layi ba Hoto: Wikepedia
Source: Facebook

“Talakawan da su ka zabi Buhari tun farko, su ne na ke so su biya kudin wakar shugaban kasa Buhari.” Rarara ya na ganin duk da halin da ake ciki, wannan mai yiwuwa ne.

Ya ce: “Idan dai ba za su biya kudin wakar ba, na daina yi. Su za su biya kudin wakar ba Buhari.”

A tattaunawarsa da 'yan jaridar, mawakin ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta taka rawar gani a bangarori da-dama, sai dai ba iya ambatar irin nasarorin da aka samu ba.

Shi dai Dauda Rarara ya yi suna a siyasa, wasu lokutan ya kan yi wa ‘yan adawar gwamnatin APC habaici da shagube, har a ji ya fito ya na zaginsu a cikin wasu wakokinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel