1448AH: Gwamna Abba Ya Ba da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci a Jihar Kano

1448AH: Gwamna Abba Ya Ba da Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci a Jihar Kano

  • Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ayyana ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026, a matsayin ranar hutu
  • Gwamnatin ta bayyana cewa ta ba da hutu ga ma'aikata ne domin bikin shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da hutun domin girmama kalandar Musulunci, aka bukaci al’umma su yi addu’o’in domin zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026, a matsayin ranar hutun aiki domin bikin sabuwar shekarar Musulunci, wato 1 ga Muharram, 1448 bayan Hijira.

Sanarwar na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 15 ga Yuni, 2026, wadda Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano ya fitar.

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yana amsa gaisuwa a fadar gwamnati Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba ya amince da hutun sabuwar shekara

Kara karanta wannan

An kuma dage shari'ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa takardar ta bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da hutun domin nuna muhimmancin kalandar Musulunci.

Gwamna Abba ya amince da hutun ne domin ci gaba da bin al’adar da jihar Kano ta dade tana yi na tunawa da farkon sabuwar shekarar Musulunci.

Sanarwar ta ce:

“Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da ayyana ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026 (1 ga Muharram, 1448AH), a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci.”

An ja hankalin musulmin jihar Kano

Gwamnatin ta bukaci ma’aikata da sauran al’umma su yi amfani da wannan dama wajen yin nazari kan rayuwarsu tare da yin addu’o’i domin dorewar zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaba da wadata a jihar Kano da Najeriya baki daya.

Takardar ta samu sa hannun Safiyya Ali Suleiman, Daraktar Gudanarwa da Ayyuka na Musamman, a madadin Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Da wannan sanarwa, dukkan ofisoshi da cibiyoyin gwamnati a fadin jihar za su kasance a rufe ranar Talata domin bai wa ma’aikata da mazauna Kano damar gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci.

Kara karanta wannan

Muharram: Sarkin Musulmi Ya Umarci Al'umma kan Duba Jinjirin Watan Sabuwar Shekara

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dalilin ba da hutun shekarar musulunci

Sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH za ta fara ne idan an ga jinjirin watan Muharram, wanda yana daga cikin watanni masu alfarma a addinin Musulunci.

Bisa haka ne gwamnatin Abba Kabir ta ba da hutun gobe Talata domin girmama sabuwar shekarar musulunci da kuma bai wa ma'aikatan Kano hutu domin murnar zagayowar wannan lokaci.

Gwamna Abba ya saki kudin auren gata

A wani labarin, kun ji cewa kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa domin gudanar da auren gata na ma'aurata 1,500.

Ya bayyana cewa za a kashe kusan N1m a kan kowane ma'aurata domin samar musu da kayan gida da suka haɗa da gado, katifa, zanen gado, matashin kai, kujeru da kayan abinci.

Sheikh Daurawa ya tabbatar da cewa tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ware Naira biliyan 1.5 domin gudanar da wannan aure cikin nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262