Latest
Wasu 'yan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai harin ta'addanci a jihar Yobe. 'Yan ta'addan sun hallaka wani dan sa-kai tare da kona gidaje.
Kotun kolin Najeriya ta shirya yanke hukunci kan taƙaddamar da aka jima ana yi game da batun mayar da Al-Mustapha Jokolo kan kujerar sarkin Gwandu.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai shirin da wasu 'yan siyasa ke yi na jawo tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya sake neman kujerar a zaben 2027 mai zuwa.
Alhaji Attahiru Bafarawa ya musanta shiga SDP, yana mai cewa labaran ba su da tushe. Ya shaida cewa yanzu ya mayar da hankali kan gina rayuwarsa a wajen siyasa.
Wata majiya ta tabbatar da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara shirin nada jakadun kasar a kasashen waje domin karfafa alakar diplomasiyya a tsakaninsu.
Gwamnan jihar Jigawa ya kai ziyarar gani da ido kan yadda shirin raba abinci na watan azumin Ramadan ke guduwa. Gwamnan ya nuna damuwa kan abin da ya gani.
Natasha Akpoti Uduaghan, Sanatar Kogi ta Tsakiya da majalisar dattawa ta dakatar na tsawon watanni shida ta kai karar batun gaban kungiyar 'yan majalisun duniya.ssss
Yan kasuwar man fetur sun bayyana cewa za su sauke farashin man fetur kasa da na matatar Dangote. Hakan na zuwa ne bayan mai ya sauka a kasuwar duniya.
Kotun Adamawa ta dage shari’ar da ke kalubalantar kafa Masarautar Fufore. Lauyan masu kara ya nemi karin lokaci don martani ga takardar da gwamnatin jiha ta gabatar.
Masu zafi
Samu kari