Sabon Rikici Ya Barke a SDP bayan El Rufa'i Ya Koma Cikin Jam'iyyar

Sabon Rikici Ya Barke a SDP bayan El Rufa'i Ya Koma Cikin Jam'iyyar

  • Rahotanni na nuni da cewa shugaban SDP na jihar Kogi ya bukaci a yi watsi da wani gangamin jam’iyyar da wasu ke shirin yi
  • Shugaban ya zargi wasu da kokarin haddasa rudani bayan shigowar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai jam’iyyar
  • A karkashin haka, shugaban ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da hukumomin tsaro su hana gangamin da aka tsara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi -'Yan sa'o'i bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shiga jam’iyyar SDP, rikici ya barke a jam’iyyar reshen jihar Kogi.

Shugaban SDP na jihar, Moses Peter Oricha, ya bukaci jama’a da hukumomin tsaro da su yi watsi da wani gangami da wasu ke shirin gudanarwa.

SDP Kogi
Rikici ya barke a SDP bayan sauya shekar El-Rufa'i. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

Leadership ta wallafa cewa Oricha ya bayyana cewa wasu da ya kira da “mambobin bogi” na kokarin yin taron ne domin kawo rudani a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

SDP: An zargi gwamnan APC da neman marin shugaban jam'iyyar El Rufa'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban SDP a jihar Kogi ya yi korafi

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Oricha ya bayyana cewa wasu gungun mutane na shirin gudanar da wani taron jam’iyyar a ranar 12 ga Maris, 2025.

Oricha ya ce:

“Na samu labari cewa wasu mutane da ba a san su ba suna ikirarin cewa su mambobin SDP ne a Kogi kuma suna shirin gudanar da taro a ranar Laraba.
"Wannan ba wai kawai abin dariya ba ne, har ma yana da hatsari a cikin tafiyar dimokuradiyya.”

Ya kuma yi zargin cewa wasu ne ke daukar nauyin wadannan mutane da nufin haddasa rikici a jam’iyyar.

Oricha ya kara da cewa:

“Wadannan mutane ba su da wani tasiri a jam’iyyarmu. Sun fito ne kawai da manufar kawo rudani da ruguza jam’iyyar da muka sha wahalar ginawa.”

Oricha ya nemi taimakon jami'an tsaro

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa a SDP ya fadi yadda aka jawo El Rufai daga APC

Shugaban jam’iyyar ya ce ya riga ya rubuta takarda ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da Sashen Tsaron Farin Kaya (DSS) da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda domin hana taron.

A cewar Moses Peter Oricha:

“Ina so a sani cewa ni ne halastaccen shugaban SDP a Kogi, kuma ba za mu bari wasu ‘yan tsiraru su lalata mana jam’iyya ba.
"Wannan taro da ake shirin yi ba shi da wata madafa a dokokin jam’iyyar.”

Oricha ya bayyana cewa an gudanar da sahihin taron jam’iyyar a jihar Kogi a ranar 9 ga Afrilu, 2022, kuma hakan ne ke kan doka har zuwa 2026 bisa tsarin jam’iyyar.

Jam'iyyar SDP ta bukaci mabiya su yi hakuri

Shugaban jam’iyyar ya bukaci dukkan magoya bayan SDP a jihar Kogi da su yi watsi da duk wani labari da ke cewa za a gudanar da sabon gangamin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

An fara: Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan tafiyar El Rufa'i a jam'iyyar SDP

Ya ce:

“Ina kira ga magoya bayan SDP da su yi watsi da duk wani shiri na karya da ake yadawa. Ba za a yi wani taro a wannan shekara ba har sai zuwa Afrilu 2026.”
SDP a Kogi
Wasu jagororin SDP a Kogi. Hoto: Legit
Asali: Original

El-Rufa'i zai hada kan 'yan adawa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna da ya koma SDP ya ce zai hada kan 'yan adawa a Najeriya.

Nasir El-Rufa'i ya ce daga yanzu har zuwa babban zaben shekarar 2027 zai cigaba da kalubalantar jam'iyyar APC a dukkan zabuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng