Yan Bindiga Sun Shiga Abuja da Bindigogi, Sun Sace Sarki da Jikokinsa

Yan Bindiga Sun Shiga Abuja da Bindigogi, Sun Sace Sarki da Jikokinsa

  • Rahotanni na nuni da cewa wasu 'yan bindiga sun sace Hakimin Dnako, HRH Etsu Yuda Garba, da jikokinsa biyu a birnin tarayya Abuja
  • Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa 'yan ta'addar sun sace wasu mutum biyar daga gidaje daban-daban a cikin dare yayin harin
  • Mutanen yankin sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi harbi a yankin domin tsoratar da mutane kafin su samu damar tserewa daga wajen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu 'yan bindiga sun afka garin Dnako da ke yankin Bwari a Abuja inda suka sace Hakimin garin, HRH Etsu Yuda Garba, da jikokinsa biyu,.

Rahotanni sun nuna cewa jikokin da aka sace su ne Ephraim da Philemon kuma an hada da wasu wasu mutane biyar.

Kara karanta wannan

"Mun ba ku lokaci," An tura motocin buldoza, sun rusa gidajen mutane da azumi a Abuja

Abuja
Yan bindiga sun sace sarki a Abuja. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Rahoton Daily Trust ya wallafa cewa 'yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 12:03 na dare, dauke da manyan bindigogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin, Tanko Baba, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa maharan sun kai hari kan gidaje hudu kafin daga bisani su kutsa gidan hakimin su yi awon gaba da shi.

Yadda 'yan bindiga suka kai hari Abuja

Shaidar gani da ido mai suna Tanko Baba ya ce 'yan bindigar sun shigo garin ne cikin shiri, inda wasu daga cikinsu suka sanya kayan sojoji domin rudar jama’a.

Trust Radio ya wallafa cewa Tanko Baba ya ce bayan sun kutsa gidan hakimin, sun nufi dakunan jikokinsa suka tasa keyarsu ba tare da wata-wata ba.

Haka zalika, an sace wani mutum mai suna Nicholas, wanda ke dawowa daga asibiti bayan matarsa ta haihu lokacin da maharan suka cafke shi.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

‘Yan bindiga sun tsere bayan kai hari

Shaidu gani da ido sun ce 'yan bindigar sun dauki sama da mintuna 30 suna barna kafin daga bisani su yi harbe-harbe su tsoratar da jama’a yayin da suke tserewa da mutanen da suka sace.

Duk da kokarin jami’an tsaro na bin sahun su, ba a samu ceto wadanda aka sace ba har zuwa yanzu.

An bukaci gwamnati ta dauki mataki

Wani jami'in ‘yan sanda da ke Bwari ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce karin bayani na hannun rundunar ‘yan sandan Abuja.

Har ila yau, kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ba ta amsa kiran manema labarai ba a lokacin hada wannan rahoto.

A baya-bayan nan, yankin Bwari na fama da hare-haren 'yan bindiga, lamarin da ke kara tayar da hankalin mazauna yankin.

Saboda haka, jama’a sun bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya dauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kai hari Borno, sun yi barna kafin isowar sojoji

"yan sanda
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An harbe dan bindiga Gwamna a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar harbe wani kasurgumin dan bindiga a Katsina.

Dan bindigar da aka kama mai suna gwamna ya shahara da kai hare hare da kama mutane yana karbar kudin fansa a Arewa ta Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng