Tinubu Zai Nada Mukamai, Za a Tura Jakadu a Kasashen Waje bayan Watanni 18

Tinubu Zai Nada Mukamai, Za a Tura Jakadu a Kasashen Waje bayan Watanni 18

  • Gwamnatin Najeriya ta fara motsawa a kan batun nada jakadun da za zu wakilce ta a kasashen ketare sama da 100
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara binciken wadanda za su jagoranci ofisoshin jakadancin kasar bayan watanni 18
  • Matakin na zuwa bayan guna-guni a kan rashin samar da wakilan Najeriya da za su kula da diflomasiyyar kasar a waje
  • Daga cikin matakan da aka fara dauka, akwai tantance wadanda ake sa ran Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin jakadu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abua - Gwamnatin Najeriya ta fara tantance mutanen da za su jagoranci ofisoshin jakadancin kasar guda fiye da 100 a kasashen waje.

Haka kuma ana sa ran sanar da sunayen sababbin jakadun da zarar an kammala tantance su nan ba da dadewa ba.

Kara karanta wannan

Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa

Tinubu
Gwamnati za ta nada jakadu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wata majaiya ta sanar da Kafar Reuters cewa wannan mataki yana zuwa ne bayan watanni 18 da Shugaba Bola Tinubu ya sauke dukkannin jakadun Najeriya a farkon mulkinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya na gudanar da harkokin diflomasiyya ba tare da jakadu ba tun daga Satumba 2023, abin da ya haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin diflomasiyya.

Dalilin Tinubu na jinkirin nada jakadu

A baya, Ministan harkokin wajen Najeriya ya bayyana cewa rashin kudi ne ya kasance babban dalilin jinkirin nada sababbin jakadun kasar.

A cewar wani majiyar gwamnati, batun rashin jakadun yana cikin shawarwarin da ake yi a matakai daban-daban na gwamnati, kuma har an fara daukar mataki.

Gwamnatin Tinubu ta fara binciken nada jakadu

A wannan lokaci, rundunar tsaron kasar nan ta fara gudanar da bincike a kan wadanda ake shirin nadawa a matsayin jakadun kasar.

Tinubu
Gwamnati ta fara tantance jakadu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wannan mataki yana cikin kokarin tabbatar da cewa wadanda za a nada sun cika ka'idojin da suka dace a matsayin wakilan Najeriya a kasashen waje.

Kara karanta wannan

Saukaka sufuri: Za a samar da motoci masu aiki da lantarki 10,000 a Arewa

Rundunar tsaro ta raba rahotanni na binciken da ta gudanar ga hukumomin da suka dace a cikin fadar shugaban kasa da majalisar dokokin Najeriya.

Gwamnatin Tinubu za ta nada jakadu a kasashe

Jinkirin nada sababbin jakadun ya janyo damuwa a tsakanin kasashen waje da ke da alaka da Najeriya, kuma sun shaidawa hukumomin kasar nan hakan.

Wani tsohon jakadan Najeriya wanda ya bayyana ra'ayinsa game da wannan batu, ya ce an sanar da shi cewa rashin jakadun na daga cikin abin da Tinubu tattauna da shugabannin wasu kasashen waje.

A cikin wadannan tattaunawar, an bai wa kasashen wajen tabbacin cewa za a nada sababbin jakadun nan ba da jimawa ba.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan nadin jakadu

A wani labarin, mun wallafa cewa babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin waje, Ademola Oshodi, ya ba da tabbacin cewa shugaba Bola Tinubu zai nada sababbin jakadun Najeriya.

Kara karanta wannan

Cibiya ta binciko abin da ya sa jami'o'in ketare suka yi wa na Najeriya nisa

Oshodi ya bayyana cewa gwamnati ta kammala shirin nada sababbin jakadun, kuma yanzu haka majalisar tarayya za ta fara tantance su domin amincewa da su, gabanin a sanar da sunayensu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng