Sauki Na Tafe: 'Yan Kasuwa za Su iya Sauke Farashin Fetur Kasa da na Dangote

Sauki Na Tafe: 'Yan Kasuwa za Su iya Sauke Farashin Fetur Kasa da na Dangote

  • Farashin litar man fetur da ake shigowa da shi Najeriya ya ragu zuwa N774 wanda zai iya rage farashinsa zuwa N800 a kasuwa
  • Hakan na zuwa ne yayin da wasu 'yan kasuwa suka koma shigo da fetur daga kasashen waje maimakon saye a matatar Dangote
  • Farashin mai yana ci gaba da faduwa a duniya, lamarin da zai iya jawo Dangote ya kara rage farashin sa don ya jawo kwastomomi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yayin da farashin man fetur ke kara saukowa a Najeriya, ‘yan kasuwar mai sun bayyana cewa farashin litar mai na iya dawowa N800.

Rahotanni sun nuna cewa farashin shigo da litar man fetur daga kasashen waje ya ragu zuwa N774.72, wanda ke nuna ragin kusan N50 idan aka kwatanta da N825 na matatar Dangote.

Kara karanta wannan

'Asara ne': Dillalan mai sun koka kan rage farashin fetur, sun kawo mafita mai ɗorewa

Gidan mai
Ana hasashen farashin mai zai kara sauka a Najeriya. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan canji na iya haifar da matsin lamba a kasuwar mai, inda ‘yan kasuwa ke kara komawa ga man da aka shigo da shi daga waje saboda farashinsa ya fi sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alakar 'yan kasuwa da matatar Dangote

A cewar ‘yan kasuwa, matsalar farashi ta sa da dama daga cikinsu sun daina sayen man Dangote, suna maida hankali kan mai da suka shigo da kansu daga waje.

Farashin jigilar litar mai daga matatar Dangote yana N825, amma idan aka kara haraji da sauransu, zai kai kimanin N834.

Haka zalika sun ce wasu manyan rumbunan ajiya irin su AA RANO, WOSBAB da AITEO sun saukar da farashin su zuwa tsakanin N830 da N832.

Ana hasashen rage farashin man Dangote

Masana sun bayyana cewa idan wannan yanayi ya ci gaba, matatar Dangote na iya rage farashinta domin ta jawo kwastomomi.

Kara karanta wannan

'Muna cikin tashin hankali': Daruruwan mata sun fita zanga zanga a jihar Benuwai

Wani kwararre a bangaren mai da iskar gas, Olatide Jeremiah ya bayyana cewa:

"‘Yan kasuwa sun fi son sayen mai daga rumbunan ajiya masu zaman kansu saboda farashin su ba ya yawan canzawa."

Ya kara da cewa wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suka saye mai daga Dangote a baya suna sayarwa ba tare da riba ba.

“A halin yanzu, babu cunkoso a wuraren sayar da mai a matatar Dangote saboda ‘yan kasuwa sun koma sayen mai daga wuraren da suka fi araha.”

Sai dai kuma Legit ta rahoto cewa Dangote ya bukaci wadanda suka saye mai a wajensa da su koma domin ya rage musu kudin da suka saya a tsohon farashi don kaucewa faduwa.

PETROAN ta koka da yawan sauya farashi

A halin da ake ciki, kungiyar ‘yan kasuwar mai ta PETROAN ta bayyana cewa yawan sauya farashin mai yana jefa su cikin asara.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya kama hanyar ƙara araha, sauƙi zai lulluɓe ƴan Najeriya

Kungiyar ta bukaci a sanya doka da za ta tabbatar da cewa ba za a rika sauya farashin mai ba sai bayan watanni shida domin kwanciyar hankali a kasuwa.

Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur, ana ci gaba da fuskantar matsalolin farashi sakamakon sauyin kasuwar duniya da kuma sauyin farashin Dalar Amurka.

Gidan mai
Mutane na sayen fetur a gidan mai. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Za a gina matatun mai 3 a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta amince da kudirn kafa wasu sababbin matatun man fetur.

Hakan na zuwa ne bayan attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya kammala matatar mai da ya fara ginawa a jihar Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng