Jami'an Tsaro Sun Rufe Ƙofa, An Hana Gwamna Shiga Zauren Majalisar Dokoki

Jami'an Tsaro Sun Rufe Ƙofa, An Hana Gwamna Shiga Zauren Majalisar Dokoki

  • Rikicin siyasar jihar Ribas ya ƙara ɗaukar sabon salo yayin da aka hana Gwamna Siminalayi Fubara shiga zauren Majalisar Dokoki
  • Fubara tare da tawagarsa sun isa Majalisar yau Laraba, 12 ga watan Maris, 2025 amma bisa mamaki suka tarar da ƙofofin shiga a rufe
  • Jami'an tsaron da ke gadin Majalisar sun bayyana cewa sun hana gwamnan shiga ne saboda bai turo sanarwar zuwansa a hukumance ba
  • Shi dai Mai girma Fubara ya musanta wannan batu, ya na mai ikirarin cewa sai da ya sanar da 'yan majalisar cewa zai hallara gabansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara ya gamu da tangarɗa yayin da ya isa harabar Majalisa Dokoki domin amsa gayyatar da suka masa.

Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo da ya faru shi ne gwamnan ya tarar da ƙofar shiga harabar Majalisar a rufe yau Laraba, 12 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan Jigawa ya kai ziyara wajen raba abinci, ya gano abin mamaki

Gwamna Fubara.
An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin jihar Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Wakilan jaridar Channels tv sun lura cewa jami’an tsaro da ke gadin majalisar ne suka kulle ƙofofin lokacin da ayarin motocin gwamnan ya iso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin hana Gwamna Fubara shiga majalisa

Jami’an tsaron da ke bakin ƙofar sun bayyana cewa majalisa ba ta samu sanarwa a hukumance daga mai girma gwamnan kan batun zuwansa ba.

A cewarsu, wannan ne babban dalilin da ya sa suka hana shi shiga zauren Majalisar dokokin, rahoton Daily Trust.

Sai dai Gwamna Fubara ya musanta hakan, yana mai cewa ya riga ya aika da wasiƙa zuwa ga Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, kuma ya yi ƙoƙarin kiransa a waya tun ranar Talata.

Fubara, wanda ke sanye da farar riga da jar hula, ya isa Majalisar ne tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Edison Ehie, da sakataren gwamnati, Dr. Tammy Danagogo.

Abin da ya faru bayan Fubara ya isa Majalisa

Lokacin da ya isa Majalisar da safiyar yau Laraba, an jiyo shi yana tambaya, "An kulle ƙofar ne?" kafin ya yi bayanin dalilin zuwansa.

Kara karanta wannan

"Bai mutu ba," Gwamnatin Taraba ta fadi halin da mataimakin gwamna ke ciki

Gwamnan ya bayyana cewa ya zo ne don sake gabatar da kasafin kuɗi na 2025 kamar yadda hukuncin Kotun Koli ya umarta, amma sai ya tarar da majalisar a rufe.

Ya ce tun kafin isowarsa, ya yi ƙoƙarin tuntuɓar Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, da wasu ‘yan majalisa ta waya, amma bai samu amsa ba.

Gwamna Fubara
Gwamna Fubara ya yi bayanin abin da ya kai shi Majalisar Dokoki Hoto: Sir Sim Fubara
Asali: Facebook

Gwamna ya faɗi dalilin zuwansa Majalisa

Fubara ya ce:

"Na zo nan tare da wasu mambobin majalisar zartarwa don yin abin da Kotun Koli ta umarta. Kafin isowata, na yi ƙoƙarin kiran Kakakin Majalisa da sauran ‘yan majalisa da yawa, amma ba su amsa ba.
"Na kuma rubuta wasiƙa da kai na, na aika ga Kakakin Majalisa don sanar da zuwa na. Amma abin takaici, na iske an kulle ƙofar gaba ɗaya, kuma babu wata alama da ke nuna cewa za a yi wani abu a yau."

Gwamna Fubara ya jaddada cewa ya na yin wannan ne ba don komai ba sai don al’ummar jihar Ribas, ba don wata manufa ta siyasa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zubar da hawaye a cikin taro, ya bayyana abin da ya sosa masa zuciya

APC ta yi barazanar tsige Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi barazanar tsige Gwamna Simi Fubara matukar bai yi murabus daga kujerarsa cikin sa'o'i 48 ba.

Shugaban APC na Ribas, Cif Tony Okocha, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a gidansa da ke Fatakwal.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262