Rigimar Sarauta Ta Ɓarke, An Maka Gwamna a Kotu kan Ƙirƙirar Masarautu
- A ranar Talata, 11 ga Maris, babbar kotun Adamawa da ke Yola ta yi zama kan shari'ar da ke kalubalantar kafa Masarautar Fufore
- Kotun ta dage shari’ar bayan lauyan masu kara ya nemi karin lokaci don yin martani ga wata takardar da gwamnati ta gabatar
- Gwamnatin jihar Adamawa ta kafa Masarautar Fufore tare da wasu sababbin masarautu a watan Disamba, shekarar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Babbar kotun kihar Adamawa da ke Yola ta dage sauraron karar da ke kalubalantar kafa masarautar Fufore zuwa ranar 3 ga Afrilu, 2025.
Kotun ta dage shari’ar ne bayan lauyan bangaren masu shigar da kara ya nemi karin lokaci don yin martani ga wata takarda da gwamnatin jiha ta gabatar.

Asali: Twitter
An yi ƙarar gwamna Fintiri kan ƙirƙirar masarautu
Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai shari’a Musa Usman, ya yanke hukuncin a ranar Talata, kamar yadda rahoton The Nation ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mun ruwaito cewa gwamnatin Adamawa ta ƙirƙiro Masarautar Fufore da wasu sababbin masarautu biyu, da kuma sarakunan yanka bakwai a watan Disambar 2024.
Mutum uku masu mukaman sarauta a masarautar Adamawa; Musa Halilu Ahmed, Alhaji Mustapha Dahiru Mustapha, da Alhaji Mustapha Ahmad, suka shigar da karar kalubalantar kafa masarautar Fufure.
Masu karar na ikirarin cewa kafa masarautar Fufore yana barazana ga tarihi da al’adar masarautar Adamawa, wadda ta dade a tarihin jihar.
Adamawa: Abin da ya faru a zaman kotun
A zaman kotun na Talata, lauyan masu kara, Manga Nuruddeen (SAN), ya nemi karin lokaci don su yi martani ga takardar da gwamnati ta gabatar.
Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotu, jaridar Tribune ta ruwaito Nuruddeen na cewa:
“An dage shari’ar a wancan zaman saboda gwamnati na da kwanaki bakwai don mayar da martani.”
“A yau, sun nemi karin lokaci bisa ka’idojin kotu, kuma mun amince da bukatarsu. Ba mu da wata matsala da hakan.”
Sai dai ya bayyana cewa:
“A takardar buƙatar karin lokacin, sun hada da wani bayani da ke buƙatar martaninmu, wanda ba mu samu damar dubawa ba, don haka muka nemi karin lokaci don ba da amsa.”
Mai shari’a Usman ya yanke hukunci cewa ya dage shari’ar zuwa ranar 3 ga Afrilu, 2025, domin masu kara su gabatar da martaninsu kafin a ci gaba da shari’ar.
Abin da gwamnatin Adamawa ta ce kan shari'ar

Asali: Facebook
Da yake magana da manema labarai, kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Adamawa, Afraimo Jingi, ya ce:
“Tun da fari, gwamnatin jihar ta gabatar da bukatar korar wannan kara saboda ba a shigar da ita a kan turbar doka ba.
"Amma masu karar sun sake gabatar da wata bukata, suna neman a tura wasu batutuwa zuwa Kotun Daukaka Kara, lamarin da muka kalubalanta.”
“Mun ga cewa ba a gina shari’ar yadda za a iya kai ta Kotun Daukaka Kara ba, don haka muka nemi izinin gabatar da takardar martani kan bukatarsu."
Da wannan dagewar, masu kara za su sami damar gabatar da martaninsu kafin kotu ta saurari muhimman hujjojin da ke cikin shari’ar.
Fintiri ya naɗa sababbin sarakuna 7 a Adamawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya naɗa sababbin sarakuna a masarautu bakwai da gwamnatinsa ta kirkira.
Gwamnan jihar na Adamawa, ya taya sarakunan murna, tare da yi musu fatan adalci da rikon amana a jagorancinsu.
Wannan na zuwa ne bayan kafa sababbin masarautun, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan tasirin sarautar Lamidon Adamawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng