Ramadan: Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyara Wurin Raba Abinci, Ya Gano Abin Mamaki

Ramadan: Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyara Wurin Raba Abinci, Ya Gano Abin Mamaki

  • Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya kai ziyara domin tantance yadda shirin ciyarwa na watan azumin Ramadan ke gudana
  • Mai girma Umar Namadi a yayin ziyarar ya nuna takaicinsa kan kura-kuran da ya hango ana tafkawa wajen ba jama'a abincin
  • Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci cuwa-cuwa a shirin ba, wanda aka yi domin amfanin al'umma

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kai ziyarar ba-zata zuwa wasu cibiyoyin bayar da abinci na azumin Ramadan a ƙaramar hukumar Dutse.

Gwamna Umar Namadi ya gano wasu matsaloli na rashin iya sarrafa kayayyaki da sakaci a wasu wuraren ba da abincin.

Namadi ya koka kan shirin ciyarwa a Ramadan
Gwamna Namadi ya ziyarci wuraren raba abincin Ramadan Hoto: @uanamadi
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa gwamnan ya kai ziyarar ne a ranar Talata, 11 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zubar da hawaye a cikin taro, ya bayyana abin da ya sosa masa zuciya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya gano kura-kuran rabon abinci

Duk da cewa wasu cibiyoyin sun samu yabo saboda jajircewarsu da bin tsari, an gano wasu suna gazawa wajen sarrafa kayayyakin abincin da kula da tsafta.

Shirin bayar da abinci na Ramadan, wanda majalisar zartarwa ta jihar ta amince da shi, ana sa ran zai lashe fiye da Naira biliyan 4.8.

A tsarin da aka yi, gwamnatin jiha za ta bayar da kaso 55%, yayin da ƙananan hukumomi za su bayar da kaso 45%.

An tsara wannan shiri ne domin samar da abinci ga mazauna jihar a cikin gundumomi 287 na ƙananan hukumomi 27, ciki har da masu zama a cibiyoyin gyaran hali, tashoshin mota, da kasuwanni.

Ziyarar da Namadi ya kai na da nufin tantance yadda ake aiwatar da shirin, wanda aka tsara domin amfanin marasa galihu a faɗin jihar.

A yayin duba cibiyoyin bayar da abinci da ke Dundubus, Karnaya, Gaci, da Limawa, yankunan da ke wajen garin Dutse, gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa game da kura-kuran da ya gano.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo El Rufai ya yi sallama da APC, ya burma jam'iyyar SDP

“Na yi matuƙar takaici, amma ba abin mamaki ba ne, ganin irin rashin kulawa da rashin iya tafiyar da shirin da na gani a yau."
“Ba za a amince da hakan ba cewa wasu za su nemi yin cuwa-cuwa da hana mutanenmu amfana da abin da ya kamata ya zama haƙƙinsu."

- Gwamna Umar Namadi

Gwamna Namadi ya ba da shawara

Gwamnan ya jaddada buƙatar yin gaskiya, adalci, da tsafta a rabon abincin, ya buƙaci masu alhaki kan kurakuran da aka gano da su gaggauta gyarawa.

Haka nan, Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da cewa duk cibiyoyin bayar da abinci na Ramadan suna aiki yadda ya kamata, tare da mutunta mutuncin al’umma.

Ya tabbatar wa da jama’a cewa za a ɗauki matakan gyara domin inganta yadda ake gudanar da shirin da kuma magance matsalolin da aka gano.

Gwamnan ya yi kira ga hukumomin ƙananan hukumomi da shugabannin al’umma da su ƙara kaimi wajen sa ido don tabbatar da cewa an aiwatar da shirin ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48

Gwamnan Jigawa ya rage lokutan aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya rage lokutan da ma'aikata za su riƙa yi a wurin aiki saboda azumin watan Ramadan.

Gwamna Namadi ya ɗauki matakin ne domin ba ma'aikatan damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin walwala ba tare da wata takura ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng