Kasar da ake ba 'Yan Mata da Samari Tallafi domin Samun Damar Fara Soyayya

Kasar da ake ba 'Yan Mata da Samari Tallafi domin Samun Damar Fara Soyayya

  • An kawo tsari na musamman a wata jiha a kasar Japan domin bayar da tallafi ga matasa maza da mata saboda sahale musu fara soyayya domin aure
  • Rahotanni sun nuna cewa ana ba matasa tallafin kudin idan suka yi amfani da manhajar neman aure domin fatan haduwa da wanda za su aura
  • An bayyana cewa ana daukar matakin ne a kasar domin karfafa matasa su rika aure saboda cike gibin karancin haihuwa da ake fama da shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Japan - Jihar Kochi ta ƙasar Japan ta bullo da wani shiri na bai wa matasa tallafin kudi domin su rika amfani da manhajojin neman aure a matsayin wani yunkuri na tinkarar raguwar haihuwa da ke addabar ƙasar.

A karkashin shirin, matasa masu shekaru tsakanin 20 zuwa 39 za su iya karbar kimanin dala 125 domin biyan mafi yawan kudin shiga manhajojin hada aure da gwamnati ta amince da su, ciki har da shahararriyar manhajar Tapple.

Kara karanta wannan

Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100

Sanae Takaichi a wajen taro a Japan
Firaministar kasar Japan, Sanae Takaichi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

The Independent ta wallafa cewa jami’an gwamnatin yankin sun ce wannan tallafi ya kusan yi daidai da kudin da ake biya a shekara domin amfani da irin wadannan manhajoji.

Ana karfafa neman aure a Japan

An rawaito cewa gwamnatin Kochi ta hada kai da manhajar Tapple tun watan Disamban 2025 domin karfafa amfani da hanyoyin neman aure na yanar gizo cikin tsari da inganci.

Wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa kudin shiga na shekara-shekara na irin wadannan manhajoji na kai sama da dala 125, shi ya sa aka daidaita tallafin da zai biya kudin.

Bincike ya nuna cewa a yankuna kamar Miyazaki ma sun taba gwada irin wannan shiri, amma da karamin tallafi da bai wuce rabin abin da ake biya a Kochi ba.

Fa'idar manhajar neman aure a Japan

A ƙasar Japan, manhajojin neman aure sun zama wata hanya ta gama gari da matasa ke amfani da ita wajen samun abokan zama.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: An samu baraka, Trump ya sauke shugaban sojin ruwan Amurka

Wani binciken gwamnati na shekarar 2024 ya nuna cewa kusan daya cikin hudu na masu aure da shekarunsu ba su wuce 39 ba sun hadu da abokan aurensu ne ta yanar gizo, fiye da wadanda suka hadu a wurin aiki ko makaranta.

Matsalar raguwar yawan jama’a a Japan na kara tsananta, musamman a yankunan karkara irin su Kochi, inda matasa da dama ke barin yankunan zuwa manyan birane.

Daily Star ta rahoto cewa a shekarar 2024 kadai, an samu mutuwar mutane kusan miliyan 1, fiye da wadanda aka haifa, wanda ya zama mafi girman koma baya a tarihin kididdigar kasar cikin shekaru 60.

Wani aure da aka daura a Japan
Wajen wani daurin aure a Otsuki, Kochi, Japan a 1974. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanan Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida sun nuna cewa an samu haihuwa 686,061 kacal, mafi kankanta tun shekarar 1899, yayin da adadin mutuwa ya kai miliyan 1.59.

Pantami ya yi nasiha a wajen aure

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon ministan sadarwan Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi nasiha a wajen auren 'ya'yan gwamnan Borno.

Rahotanni sun nuna cewa gwamna Babagana Umara Zulum ya aurar da 'ya'yansa guda hudu, inda manya a fadin Najeriya suka hallara.

Yayin nasiha ga ma'auratan, Sheikh Pantami ya bayyana cewa dole su rika hakuri da juna, kyautatawa juna tare da yafiya idan aka samu kuskure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng