Duk da Matsalar da Ake Fama da Ita a Najeriya, An ba Ƴan Bindiga Miliyoyin Naira da Azumi

Duk da Matsalar da Ake Fama da Ita a Najeriya, An ba Ƴan Bindiga Miliyoyin Naira da Azumi

  • Ƴan bindigar da suka sace ma'aikata masu binciken kasa sun sako su bayan an tura masu miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa
  • Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun sako mutum tara da suka sace a Ondo bayan an biya su Naira miliyan 20
  • Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda reshen jihar Ondo kan wannan ci gaban da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Bayan kwashe sama da mako guda a hannun ‘yan bindiga, masu binciken ƙasa guda tara da aka sace a Ilu Abo da ke ƙaramar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, sun samu ‘yanci.

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da su sun sako su ne a daren Talata bayan karɓar Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga Abuja da bindigogi, sun sace sarki da jikokinsa

Taswirar Ondo.
Yan bindiga sun sako ma'aikatan binciken ƙasa da suka sace bayan an biya N20m Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda aka sace masu binciken ƙasa

An sace waɗannan masu binciken ƙasa ne a ranar Talata, makon da ya gabata, yayin da suke gudanar da ayyukansu a wani filin gini a yankin, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan bindigar, da suka farmake su ɗauke da mugayen makamai, sun yi awon gaba da su ba tare da barin wata alama ba.

Bayan sace su, ‘yan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin su sako su.

Wannan ya jefa dangi da abokan aiki na waɗanda aka sace cikin matuƙar damuwa, inda suka nemi gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar ceto su.

An biya ƴan bindiga N20m kafin sako su

Wani daga cikin ‘yan uwan waɗanda aka sace, Fasto Ajibade Owolanke, ya tabbatar da cewa an sako su ne bayan an tura wa ƴan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 20.

Ya bayyana cewa wasu daga cikinsu sun riga sun koma gida, yayin da wasu ke asibiti ana ci gaba da kulawa da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa

A cewarsa, mutanen sun fuskanci azaɓa mai tsanani da zama a mawuyacin hali a hannun ‘yan bindigar, kuma sun sha baƙar wahala kafin a sako su, rahoton Leadership.

Mata sun yi zanga-zanga a Ondo

Bayan sace mutanen, mata ‘yan kasuwa daga yankin sun yi tattaki zuwa ofishin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, suna neman ya shiga tsakani don ganin an ceto su.

Sun nuna damuwa kan yadda satar mutane ke ƙaruwa a yankin, suna mai cewa kasuwancinsu da rayuwarsu na cikin barazana.

Yan sanda.
An biya yan bindiga kuɗin fansar mutum 9 a jihar Ondo Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya.

Sace mutane don neman fansa na ƙaruwa a Najeriya, inda mutane da dama ke shan wahala a hannun ‘yan bindiga.

An ceto malamai da 'yan bindiga suka sace

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaron haɗin guiwa sun samu nasarar ceto limaman coci biyu da aka yi garkuwada su a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

An kama babban 'dan bindiga da ya tara miliyoyin Naira a daji

'Yan bindiga sun sace fastocin; Abraham Samman da Matthew Dusami, a ranar 21 ga Fabrairu a kauyen Gwaida Mallam amma yanzu sun shaƙi iskar ƴanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng