Ana tsaka da Batun Sauya Sheƙar El Rufai, Ƴan Majalisa 4 Sun Fice daga PDP da LP
- Jam'iyyar APC ta samu rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Edo da ƴan Majalisa huɗu suka sauya sheƙa daga PDP, LP zuwa APC mai mulki
- Ƴan Majalisar sun tabbatar da komawa APC ne yayin da suka kai ziyara sakatariyar jam'iyyar da ke Birnin Benin da safiyar Laraba
- Shugaban APC na reshen jihar Edo, Jarret Tenebe ya tarbi ƴan Majalisar tare da ba su tabbacin cewa sun zama ɗaya da kowane 'dan jam'iyya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Jam’iyyar APC mai mulki, a ranar Laraba ta samu rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Edo bayan sauya sheƙar ‘yan majalisa hudu daga PDP da LP.
Wannan sauya sheka ta ƴan Majalisa huɗu na zuwa ne a lokacin da ake ta surutu da ce-ce-ku-ce kan ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP.

Asali: Twitter
Da wannan ci gaba, APC ta zama mafi rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Edo da mambobi 13 yayin da PDP ke da mambobi 11, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan Majalisa 4 da suka koma APC
‘Yan majalisar da suka koma APC a jihar Edo sun haɗa da; Hon. Donald Okugbe mai wakiltar Akoko Edo II da Hon. Bright Iyamu, mai wakiltar Orhionmwon ta Kudu II
Sauran su ne Hon. Richard Edosa, mai wakiltar Oredo ta Yamma da kuma Hon. Sunday Ojezele, wanda ke wakiltar mazaɓar Esan ta Kudu maso Gabas.
Ƴan Majalisar sun ziyarci sakatariyar APC da ke Benin City, inda aka karɓe su hannu bibiyu.
Shugabannin APC na jihar Edo karkashin jagorancin shugaban jam'iyya, Jarret Tenebe, ne suka karɓi masu sauya sheƙar a hukumance.
Dalilan ƴan Majalisa na komawa APC
Hon. Richard Edosa, wanda ya yi magana a madadin sauran ‘yan majalisar, ya ce:

Kara karanta wannan
Wike ya kara rura wutar rikicin Rivers, ya fadi abin da zai faru idan an tsige Fubara
"Idan gida ya dare, ba zai iya tsayawa da ƙafafunsa ba. Mun ga yadda jam’iyyunmu ke cikin rikici, don haka muka yanke shawarar bin tafiyar Gwamna Monday Okpebholo don ci gaban jihar Edo.
"Muna da niyyar yin aiki tare da mai girma gwamna domin bunƙasa jiharmu ta Edo.”
APC ta yi maraba da sauya shekar
Mukaddashin shugaban APC, Jarret Tenebe, ya bayyana sauya sheƙar ‘yan majalisar a matsayin muhimmin ci gaba ga jam’iyyar.
Ya tabbatar da cewa za su sami dukkan haƙƙoƙin da sauran mambobin jam’iyyar ke da su ba tare da nuna wariya ba.
Daily Post ta ruwaito Tenebe na cewa:
"Waɗannan ‘yan majalisar sun fahimci cewa APC ce hanyar da za ta kawo ci gaba a Edo da Najeriya baki ɗaya. Sun yi nazari a kan manufofin jam’iyyar, jajircewar Gwamna Okpebholo, da kuma manufarsa ta kyautata rayuwar al’ummar Edo..
“Sauya sheƙa ba abu bane mai sauƙi, ya na buƙatar jarumta da hangen nesa. Muna yaba wa waɗannan ‘yan majalisar da suka yanke shawarar hada kai da mu don gina tattalin arziki mai ƙarfi, inganta ilimi, da tabbatar da zaman lafiya.”
Rikici ya ɓarke a PDP ta Kudu maso Kudu
A wani labarin, kun ji cewa PDP a Kudu maso Kudu ta tsinci kanta cikin rikici bayan wani taro da Cif Dan Orbih, ya shirya a garin Benin, jihar Edo.
Manyan kusoshin jam’iyyar PDP sun caccaki wannan taro da aka gudanar, a cewarsu shirya wannan taro ya saɓa wa ƙa'iadar jam'iyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng