Wike Ya Kara Rura Wutar Rikicin Rivers, Ya Fadi Abin da Zai Faru idan an Tsige Fubara

Wike Ya Kara Rura Wutar Rikicin Rivers, Ya Fadi Abin da Zai Faru idan an Tsige Fubara

  • Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya taɓo batun shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara a majalisar dokoki
  • Nyesom Wike ya bayyana cewa ba laifi ba ne idan ƴan majalisar dokokin jihar sun tsige Gwamna Fubara idan sun same shi da laifi
  • Wike ya nuna babu wani abu da zai faru ko da ƴan majalisar ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule sun yi waje da Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya yi magana kan rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.

Nyesom Wike ya bayyana cewa babu abin da zai faru idan majalisar dokokin jihar, wacce Martins Amaewhule ke jagoranta, ta tsige magajinsa, Gwamna Siminalayi Fubara.

Wike ya yi magana kan shirin tsige Gwamna Fubara
Wike ya ce babu abin da zai faru idan an tsige Gwamna Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta ce Wike ya bayyana hakan lokacin da yake magana da manema labarai a Abuja a ranar Laraba, 12 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

'Ku tsige shi': Minista ya bukaci majalisa su tuge yaronsa daga kujerar gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta jiƙawa Gwamna Simi Fubara aiki

A ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, 2025, Kotun Koli ta yanke hukunci kan rikicin siyasa da ke gudana a jihar Rivers, wacce ke cikin yankin Kudancin Najeriya mai arziƙin mai.

A hukuncin da Mai Shari’a Emmanuel Akomaye ya gabatar, kwamitin alkalan kotun guda biyar sun yi watsi da ƙarar da Fubara ya shigar yana ƙalubalantar halaccin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin shugabancin Martins Amaewhule.

Bayan yanke hukuncin, kotun ta umarci Amaewhule da sauran ƴan majalisar da su ci gaba da zamansu ba tare da wani jinkiri ba.

Haka nan kuma, Kotun Koli ta soke zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar a ranar 5 ga watan Oktoba, 2024, tana mai bayyana shi a matsayin zaɓen da bai halasta ba.

Daga bisani, Gwamna Fubara ya bayyana cewa zai aiwatar da hukuncin kotun dari bisa dari, tare da umartar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) da ta fitar da sababbin tsare-tsare don gudanar da sabon zaɓe.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun rufe ƙofa, an hana gwamna shiga zauren Majalisar Dokoki

Me Wike ya ce kan tsige Gwamna Fubara?

Wike wanda a yanzu shi ne ministan Abuja, ya ce ba kuskure ba ne idan ƴan majalisar sun yanke shawarar tsige Gwamna Fubara

Tsohon gwamnan ya ce ba laifi ba ne idan an tsige Gwamna Fubara saboda wasu dalilai da suka haɗa da rashin biyan albashin ƴan majalisun na tsawon watanni, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Idan mutum ya aikata abin da zai sa a tsige shi, to menene matsalar? Shin laifi ne? Kundin tsarin mulki ya tanadi hakan. Shin ni mamba ne a majalisar?
“Idan mutum ya karya kundin tsarin mulki, kuma majalisa ta ga ya dace a tsige shi, babu laifi a kan hakan."
“Na ji wasu na cewa idan aka tsige shi, za a samu tashin hankali da karya doka da oda. Wannan ba gaskiya ba ne! Babu abin da zai faru."

- Nyesom Wike

An hana Gwamna Fubara shiga majalisa

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnan Jigawa ya kai ziyara wajen raba abinci, ya gano abin mamaki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gamu da cikas bayan ya yi yunƙurin shiga harabar majalisar dokoki.

Gwamna Fubara ya tarar da ƙofar shiga harabar majalisar a kulle bayan ya je domin sake gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng