Hankalin Jama'a Ya Tashi: Ƴan Bindiga Sun Fara Kafa Sansanoni a Garuruwan Katsina

Hankalin Jama'a Ya Tashi: Ƴan Bindiga Sun Fara Kafa Sansanoni a Garuruwan Katsina

  • 'Yan bindiga sun kafa sansani a wasu garuruwan jihar Katsina, inda suke kai hare-hare tare da tilasta jama'a yin kaura daga gidajensu
  • Rahotanni sun ce 'yan bindiga sun kafa sansani a Bakori da Mununu, sannan suna kokarin kafa sansani a Tafoki don mamaye garuruwa hudu
  • Gwamnatin Katsina ta ce tana aiki da jami'an tsaro, har ma da jiragen yaki domin dakile hare-haren 'yan bindiga, sai dai har yanzu ba nasara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Wasu majiyoyi daga jihar Katsina sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kafa wani sabon sansani a yankin ƙaramar hukumar Bakori.

Ana zargin cewa wasu daga cikin 'yan bindigar na ƙoƙarin kafa wani sabon sansani a cikin wani daji da ke kusa da garin Tafoki na yankin ƙaramar hukumar Faskari.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

'Yan bindiga sun fara kafa sansanoni a garuruwan Katsina, mutane sun fara tserewa
Rahoto ya nuna yadda 'yan bndiga ke mamaye garuruwan jihar Katsina. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda 'yan bindiga ke tarewa a Katsina

Saboda wannan barazana, jama’ar yankunan da abin ya shafa sun fara tserewa daga gidajensu domin tsira da rayukansu da na iyalansu daga 'yan bindiga, inji rahoton BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya jefa mutane cikin firgici, duk kuwa da iƙirarin hukumomin tsaro na cewa suna kokarin ganin bayan 'yan bindiga a yankin.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa matsalar hare-haren 'yan bindiga ta ƙara ƙamari a 'yan kwanakin nan.

A cewarsa, 'yan bindigar sun canza salo, domin tun farko suna kai hare-hare ne da daddare, amma yanzu sun fara fitowa da tsakiyar rana.

'Yan bindiga sun kafa sansani a Mununu

Mazaunin ya bayyana cewa jama’a da dama sun rasa dukiyoyinsu, wanda ya tilasta wasu takawa a kasa domin fita da garuruwansu saboda rashin kudin mota.

Yanzu haka dai an sanar da cewa, 'yan bindigar sun kafa sansani a kauyen Mununu, daga nan ne suke fita suna addabar al'umma da kwace dukiya a yankin Bakori.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun kai hari makaranta ana suhur a Katsina, sun yi kisan kai

A cewar wani mazaunin yankin Mununu, tun watan da ya gabata ne aka fara samun yawaitar hare-hare a wannan yanki, kuma matsalar ta na ta ƙaruwa.

'Yan bindiga na shirin kafa sansani a Tafoki

An rahoto cewa wasu ƙungiyoyin sa-kai da aka kafa a yankin sun kai koke ga gwamna, amma har yanzu ba a ga wani sauyi kan tsaron ba.

A yankin Tafoki, mazauna sun bayyana cewa 'yan bindigar suna shiga cikin gari, suna kame mutane suna kai su daji domin neman kuɗin fansa.

Wani mazaunin Tafoki ya tabbatar da cewa 'yan bindigar na shirin kafa wani sansani domin su mamaye Bakori, Faskari, Funtua da Danja baki ɗaya.

Gwamnatin jihar Katsina ta yi martani

Gwamnan Katsina, Dikko Radda yayin da yayi Sallah a hanyar Kankara zuwa Sheme
Dikko Radda da tawagarsa sun yi Sallah a hanyar Kankara-Sheme, wadda ke da hatsarin tsaro. Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Kwamishinan tsaron Katsina, Dokta Nasiru Mu’azu, ya bayyana cewa jami’an tsaro suna kokarin ganin an dakile wannan matsala.

Ya ce ana amfani da jiragen yaki, sojojin ƙasa, 'yan sanda, 'yan banga da jami’an NSCDC domin yakar 'yan bindiga a yankin.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi rashin imani, sun tashi mutanen garuruwa 5 ana azumi

Kwamishinan ya ƙara da cewa ba zai bayyana duka matakan tsaro da ake ɗauka ba don gujewa bayyanawa 'yan ta’adda dabarun da ake amfani da su.

"Akwai bukatar kafa sansanin soji a shiyyar Funtua" - Maikarfe

Nura Haruna Maikarfe, mai sharhi kan lamuran yau da kullum daga karamar hukumar Funtua, ya ce ya shiga damuwa da rahoton kafa sansanin 'yan bindiga a garuruwan shiyyar.

Nura Haruna ya ce:

"Wallahi mutane suna cikin tsoro da firgici sosai, kusan kullum muna ganin shigowar 'yan gudun hijira a garin Funtua, duk sun tsero daga gidajensu don tsira da rayukansu.
"Kafa sansanoni a Mununu da ƙoƙarin kafa wani a Tafoki ya nuna cewa 'yan bindigar suna ƙara ƙarfi da samun damar mamaye ƙarin yankunan Funtua.
"Don magance wannan matsalar, ya zama dole a ƙara ƙarfin rundunonin tsaro a yankin, tare da ba su isassun kayan aiki da horo, musamman a kafa sansanin soji a shiyyar Funtua."

Kara karanta wannan

Zamfara: An hallaka hatsabibin ɗan ta'adda da aka daɗe ana nema ruwa a jallo

Maikarfe ya kuma ce akwai bukatar a tallafa wa mazauna yankunan da abin ya shafa, musamman waɗanda suka rasa matsugunansu, don rage radadin da suke fuskanta.

'Yan Tafoki sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mazauna kauyen Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina, sun kashe ’yan bindiga uku bayan harin da suka kai masu

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, ’yan bindiga dauke da manyan makamai sun afka Tafoki a kan babura kusan 100, amma ba su yi nasara ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng