Gwamnan APC Ya Tsage Gaskiyar Shirinsa Na Bin El Rufai zuwa SDP
- Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya fito fili ya yi magana kan raɗe-raɗin da ke cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APC
- Rabaren Hyacinth Alia ya musanta cewa yana shirin bin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai zuwa jam'iyyar SDP
- Gwamnan ya bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin jita-jitar, ya ce ana son ɓata alaƙarsa da shugaba Bola Tinubu ne kawai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya karyata jita-jitar da ke ce yana shirin ficewa daga APC zuwa jam'iyyar SDP.
Gwamna Hyacinth Alia ya ƙaryata jita-jitar mai cewa ya shirya tattara kayansa daga jam'iyyar APC.

Asali: Facebook
Gwamna Alia ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Tersoo Kula, ya fitar a ranar Laraba a Makurdi, cewar rahoton jaridar PM News.

Kara karanta wannan
Wike ya kara rura wutar rikicin Rivers, ya fadi abin da zai faru idan an tsige Fubara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin Gwamna Alia na shirin barin APC?
Gwamnan ya jaddada cewa bai taɓa tunanin barin jam’iyyar da ta kai shi kan mulki ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A cewarsa, mutanen da ke yaɗa irin wannan jita-jitar a kafafen sada zumunta suna ƙoƙarin haddasa rashin jituwa ne tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu.
“Irin waɗannan maganganun ba su da tushe balle makama, kuma suna nuna rashin fahimta game da irin kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninmu da shugaban ƙasa."
“Maganar cewa ina shirin komawa jam’iyyar SDP tare da Mallam Nasir El-Rufai da wasu ba komai ba ne face shaci-faɗi da babu wata hujja ta gaskiya da ke tabbatar da hakan."
“Waɗanda ke yaɗa waɗannan ƙaryace-ƙaryacen sun je sun ɗauko wani tsohon hoto daga wata ziyarar da aka yi a baya, suka sauya shi domin su yaɗa labarinsu na ƙarya."
“Bayan sun riƙa yaɗa cewa tsohon gwamnan Kaduna ya kai ziyara Makurdi, sun manta cewa irin waɗannan ziyarorin ana fitar da cikakken rahoton tsaro idan aka kawo su."
- Gwamna Hyacinth Alia
Gwamna Alia ya faɗi rawar da ya taka a APC
Gwamna Alia ya ƙara da cewa a matsayinsa na jagoran APC a Benue, ya farfado da jam’iyyar wacce ta kusa durƙushewa kafin zaɓen 2019.
“Irin yadda muke gudanar da mulki bisa gaskiya ba kawai ya ƙarfafa APC ba ne, har ma ya jefa jam’iyyun adawa cikin halin ruɗani."
“Kuma tun bayan hawana mulki, mun yi ƙoƙari wajen dawo da dangantaka mai karfi tsakanin Benue da gwamnatin tarayya, wanda hakan ya haifar da ɗimbin alfanun da suka haɗa da samun muƙamai masu tsoka ga mutanenmu."
“Goyon bayanmu ga manufofin shugaba Tinubu a bayyane yake ta hanyar muhimman shirye-shiryen ci gaba da muke aiwatarwa a faɗin jihar."
- Gwamna Hyacinth Alia
Gwamnan ya jaddada cewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga shugabancinsa ba zai yi nasara ba.
Mutanen da El-Rufai ya ziyarta kafin barin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa kafin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fice daga jam'iyyar APC, ya ziyarci wasu mutane a siyasa.

Kara karanta wannan
El Rufai ya fara tone tone, ya fallasa makarkarshiyar da gwamnatin APC da ke kullawa
Tsohon gwamnan na Kaduna ziyarci manyan ƴan siyasa kafin ya yanke shawarar komawa jam'iyyar SDP mai adawa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng