Gwamnan Yobe Ya Tuna da Matasa, Ya Gwangwaje Su 200 da Mukamai a Gwamnatinsa
- Matasa 200 sun samu gurbi a cikin gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Mai girma Gwamna Mai Mala Buni
- Mai Mala Buni ya naɗa matasan a matsayin hadimansa, domin su zo, su ba da irin tasu gudunmawar wajen ci gaban jihar
- Matasan dai an naɗa su muƙaman manyan mashawarta na musamman da mataimaka na musamman kan sadarwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da nadin sama da matasa 200 a matsayin hadimai a gwamnatinsa.
Gwamna Mai Mal Buni ya naɗa matasan a matsayin masu kula da harkokin gwamnati, manyan mashawarta na musamman, mashawarta na musamman da kuma mataimaka na musamman a ɓangaren yaɗa labarai.

Asali: Facebook
Gwamna Buni ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen suna nuna himmarsa wajen bai wa matasa damar shiga cikin harkokin mulki, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Yobe ya naɗa hadimai 200
Mai Mala Buni ya ce matakin zai sanya a ci gajiyar sababbin dabarun matasan domin inganta hanyoyin sadarwa da yaɗa manufofin gwamnati.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan, Mallam Yusuf Ali, ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗe sun yi daidai da ƙudirin gwamnatin jihar Yobe na bai wa matasa masu hazaƙa damar ba da gudunmuwa wajen ci gaban jihar.
A cewarsa, wannan naɗin da gwamnan ya yi, wanda bai taɓa yin irinsa ba a baya, wata shaida ce ta irin salon shugabancinsa wanda ke mayar da hankali kan bai wa kowa dama ya ba da irin ta sa gudunmawar a gwamnati.
Ya ƙara da cewa, ana sa ran waɗanda aka nada za su fara aiki nan take domin kawo sababbin dabaru a ƙoƙarin inganta hanyoyin sadarwar gwamnatin jihar.
Gwamna Buni ya gatanta matasan Yobe
Wannan mataki na ba matasa muƙamai na da nufin ƙarfafa su, ƙara ƙarfafa shigar matasa cikin tafiyar da gwamnati, da rage matsalar rashin aikin yi da ke addabar ɗumbin matasan jihar.
Matakin yana da muhimmanci matuƙa duba da yadda matasa ke taka muhimmiyar rawa a fannin bunƙasa al'umma.
Haka zalika, zai taimaka wajen samar da wata kafa da za ta ba matasa damar bayyana basirarsu da bayar da gudunmuwa kai tsaye ga ci gaban jihar.
Baya ga haka, gwamnatin na fatan waɗannan matasa za su zama jakadun da za su taimaka wajen yaɗa manufofi da ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa ga jama’a, musamman ta hanyar kafafen yaɗa labarai na zamani.
Da wannan matakin, Gwamna Mai Mala Buni ya kara tabbatar da cewa gwamnatinsa na aiwatar da manufofin da za su bunƙasa rayuwar matasa.
Gwamnan Yjihar obe ya samu muƙami
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya samu sabon muƙami a yankin Tafkin Chadi.
An zaɓi Gwamna Mai Mala Buni a matsayin shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin a wani taro da aka gudanar a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng