Kotu Ta Soke Belin Tsohon Hadimin El Rufai, An Kara Ingiza Keyarsa zuwa Kurkuku

Kotu Ta Soke Belin Tsohon Hadimin El Rufai, An Kara Ingiza Keyarsa zuwa Kurkuku

  • Wata kotu da ke zamanta a jihar Kaduna ta soke belin tsohon shugaban maaikatan gwamnatin Nasir El-Rufai, Bashir Sa'idu a shari'ar da ake yi da shi
  • Bayan wannan mataki, an sake tsare shi bayan sababbin bayanai sun fito a kan shari’ar da gwamnati ke yi da shi game da zargin almundahana
  • Bayan zaman kotu da aka yi a yau, an tesa keyar hadimin tsohon gwamnan inda zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali har zuwa zaman kotu na gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Wata kotu a Kaduna ta bayar da umarnin sake tsare Bashir Saidu, tsohon Shugaban Ma’aikatan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, bayan ta soke belin da aka ba shi a baya.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki matakin farko kan wadanda ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki

Bashir Saidu na fuskantar tuhume-tuhume da dama, daga ciki har da zargin rashin gaskiya a harkokin kuɗi, wanda ya jawo hankalin jama’a da masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.

An sake mayar da hadimin El-Rufa'i kurkuku
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i da hadimi a gwamnatinsa, Bashir Sa'idu Hoto: Nasir El-Rufa'i/Bashir Saidu
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa a baya, an tsare Bashir Saidu na tsawon kwanaki 50 kafin kotu ta ba shi beli, bayan ya cika dukkan sharuɗan da aka shimfiɗa masa.

Kotu ta soke belin hadimin tsohon Nasir El-Rufa'i

Daily Trust ta wallafa cewa bayan fitowar Bashir Sa'idu, ya koma harkokin siyasa a Kaduna, inda ya kasance mai tasiri musamman a jam’iyyar ADC.

Sai dai a zaman kotu na ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026 an bayyana wasu sababbin bayanai da suka sauya yanayin shari’ar, lamarin da ya sa kotu ta yanke shawarar soke belin da aka ba shi a baya.

Rahotanni sun nuna cewa sababbin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu sun taka muhimmiyar rawa wajen yanke hukuncin soke belin Bashir Saidu.

Wani makusancin Bashir Saidu da ke da masaniya kan lamarin ya tabbatar da cewa:

Kara karanta wannan

Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu

“An soke belin kuma an sake tsare shi."

An mayar da tsohon hadimin El-Rufa'i kurkuku

Bayan wannan hukunci, an mayar da Bashir Saidu gidan gyaran hali da ke Kaduna, inda zai ci gaba da zama har zuwa lokacin da za a sake zama domin ci gaba da sauraron shari’ar a wata mai zuwa.

Bashir Sa'idu zai ci gaba da zama a kurkukun Kaduna
Taswirar jihar Kaduna inda aka sake hukuncin hadimin tsohon gwamna Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lamarin ya kara daukar hankali a jihar Kaduna, musamman ganin irin rawar da Bashir Saidu ya taka a lokacin mulkin El-Rufai da kuma ci gaba da kasancewarsa cikin harkokin siyasa bayan saukarsa daga mukami.

Ana ganin cewa wannan mataki na kotu na iya yin tasiri ga yanayin siyasa a jihar, musamman a daidai lokacin da ake shirin tunkarar zabuka masu zuwa.

Ana sa ran shari’ar za ta ci gaba a watan gobe, inda bangarorin biyu za su gabatar da karin hujjoji domin tabbatar da gaskiyarsu a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗauki mataki kan buƙatar belin El Rufai, Malam zai zauna a hannun ICPC

An kai Nasir El-Rufa'i kotu

A baya, kun samu labarin cewa yau Alhamis, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Hukumar DSS na zargin Nasir El-Rufai da laifuffuka biyar da suka shafi katsalandan da leken asiri kan tattaunawar wayar tarho ta mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Wannan takun-saƙa ya samo asali ne daga iƙirarin da El-Rufai ya yi a gidan talabijin cewa ya saurari umarnin da Ribadu ya bayar na a kama shi da zarar ya sauka a Najeriya bayan ya yi balaguro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng