Latest
Alhaji Attahiru Bafarawa ya musanta shiga SDP, yana mai cewa labaran ba su da tushe. Ya shaida cewa yanzu ya mayar da hankali kan gina rayuwarsa a wajen siyasa.
Wata majiya ta tabbatar da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara shirin nada jakadun kasar a kasashen waje domin karfafa alakar diplomasiyya a tsakaninsu.
Gwamnan jihar Jigawa ya kai ziyarar gani da ido kan yadda shirin raba abinci na watan azumin Ramadan ke guduwa. Gwamnan ya nuna damuwa kan abin da ya gani.
Natasha Akpoti Uduaghan, Sanatar Kogi ta Tsakiya da majalisar dattawa ta dakatar na tsawon watanni shida ta kai karar batun gaban kungiyar 'yan majalisun duniya.ssss
Yan kasuwar man fetur sun bayyana cewa za su sauke farashin man fetur kasa da na matatar Dangote. Hakan na zuwa ne bayan mai ya sauka a kasuwar duniya.
Kotun Adamawa ta dage shari’ar da ke kalubalantar kafa Masarautar Fufore. Lauyan masu kara ya nemi karin lokaci don martani ga takardar da gwamnatin jiha ta gabatar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Ribas musamman tsakanin Fubara da Wike yayin da shugaban APC ya yi barazanar tsige gwamna.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa sun ba jama'a isasshen lokaci amma suka nuna taurin kai, ya jagoranci rusa gidaje a birnin tarayya Abuja.
CP Ibrahim Adamu Bakori ya zama sabon kwamishinan 'yan sanda a Kano tare da kudurin yakar laifuffuka da tabbatar da zaman lafiya a jihar. An samu karin bayanai.
Masu zafi
Samu kari