An Tura Sabon Kwamishinan Ƴan Sanda zuwa Kano, An Fada Masa Aikin da Zai Fara Yi
- Hukumar kula da 'yan Sanda ta amince da nadin CP Ibrahim Adamu Bakori a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano
- CP Ibrahim Bakori, wanda ya fito daga jihar Katsina, ya maye gurbin Salman Dogo, wanda aka karawa girma zuwa mataimakin Sufeto-Janar
- Shugaban hukumar PSC, DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), ya yi wa Bakori hudubar kama aiki, tare da fada masa ayyukan da zai fara yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta amince da nadin CP Ibrahim Adamu Bakori a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano.
Nadin CP Ibrahim Bakori na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar a ranar Talata.

Asali: Twitter
Kano ta samu sabon kwamishinan 'yan sanda
Bakori, wanda ya fito daga jihar Katsina, ya maye gurbin tsohon kwamishinan ‘yan sanda na Kano, Salman Garba Dogo, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa tsohon kwamishinan Kano, Salman Dogo yanzu ya samu karin girma zuwa mukamin mataimakin Sufeto-Janar (AIG.)
Kafin zama kwamishinan Kano, CP Bakori shi ne kwamishinan sashen binciken kisan kai a hukumar binciken manyan laifuffuka ta rundunar ‘yan sandan Abuja.
Kwarewar CP Bakori kafin zama kwamishinan Kano
Sanarwar ta bayyana cewa yana da kwarewa sosai a aikin ‘yan sanda, inda a baya ya jagoranci rundunar hadin gwiwa ta Bayelsa (Operation Doo Akpo) a Yenagoa.
Har ila yau, ya rike manyan mukamai kamar mataimakin kwamishinan sashen kariya na musamman (SPU) a hedikwatar ‘yan sandan Abuja.
Bugu da kari, CP Ibrahim Bakori ya kuma rike mukamin mataimakin kwamishinan sashen binciken manyan laifuka (CID) a jihohin Bayelsa da Rivers.
Ya kuma taba zama babban hadimi na Sufeto-Janar na ‘yan sanda, da kwamandan rundunar 17 ta ‘yan sandan mobal (PMF) da ke Akure.
Aikin farko da aka dorawa CP Bakori a Kano

Asali: Original
Punch ta ruwaito shugaban hukumar PSC, DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), ya bukaci sabon kwamishinan da ya tabbatar da zaman lafiya a Kano.
Ya bukaci CP Ibrahim Bakori shi da ya shiga aikinsa da zafin nama tare da mayar da hankali kan yaki da masu aikata laifuffuka da ‘yan ta’adda a fadin jihar.
DIG Argungu ya jaddada bukatar kare lafiyar al’umma, bai wa ‘yan kasuwa damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali da tabbatar da ci gaban tattalin arziki.
Ya bukaci CP Bakori da ya yi amfani da dabarun tantance wuraren da ake fama da aikata laifuka a Kano domin kawo sabuwar rayuwa ga jihar.
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sa ido kan yadda sabon kwamishinan ke gudanar da aikinsa tare da ba shi goyon baya don samun nasara.
Matsayar kwamishina kan rigimar sarautar Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamishinan 'yan sandan Kano, Salman Garba Dogo, ya bayyana shirin gudanar da aikinsa duk da rikicin sarauta a jihar. Ya jaddada cewa zuwansa Kano domin aiki ne, ba don kare muradun wani bangare ko wani tsiraru ba. CP Salman Dogo ya kuma musanta cewa yana da wata alaka da Aminu Ado Bayero, ya na mai cewa shi ma a ranar ya fara jin wannan labari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng