Latest
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya rasa wani na hannun damansa, Barista Abdullahi Nyako. Ya amsa kiran mahaliccinsa a safiyar Alhamis.
A hare-hare kusan 200 da aka kai jihar Benue, akalla mutane 5000 ne suka rasa rayukansu ta sanadiyyar barnar tsageru cikin shekaru 11, Daily Trust ta ruwaito.
Uwar Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a ranar Laraba ta kira zaman gaggawa bisa baran-baran da wasu jiga-jigan jam'iyyar sukayi da yakin neman zaben.
Lafia - A wani sabon magudi da aka bankado a aikin ma'aikatar jinkai da jin dadin al'umma, gwamnatin tarayya ta bankado makarantun karya 349 a jihar Nasarawa.
Rikicin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Alhaji Atiku.
Tubabbun mayakan Boko Haram 20 sun mutu sakamakon barkewar annobar amai da gudawa a sansanin aikin hajji inda aka ajiye kimanin su 12,000 a Maiduguri, Borno.
Biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ambaliyar ruwa ta karya gadar Maliki da ke Zaria a jihar Kaduna, mutum daya ya rasu yayin da ruwa ya wanke gonaki.
Jagororin al'umma daga jihohi 19 da birnin Abuja da suka haɗa Arewacin Najeriya, sun ce ba wanda zasu goya wa baya sai wanda zai magance matsalolin yankinsu.
Fasto Samuel Oladele kuma limamin Christ Apostolic Church (CAC) Worldwide ya ba kiristoci satar amsa a zaben Shugaban kasa, yace su bi wanda zai kare ra’ayinsu.
Masu zafi
Samu kari