Sufetan Yan Sanda Na Kasa Ya Shiga Ganawa da Manyan Jami'ai a Abuja
- Sufeja Janar na hukumar yan sandan ƙasar nan (IGP) Usman Baba, ya gana da manyan jami'ai a birnin tarayya Abuja
- Wasu bayanai sun nuna cewa taron zai tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka haɗa da zaben 2023 da cin zarafin yan sanda
- Mataimakan sufeta na ƙasa, Kwamishinonin jihohi 36 da Abuja da sauran manyan jami'ai duk sun halarci taron
Abuja - Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan ƙasar nan (IGP), Usman Alƙali Baba, ya shiga gana wa da manyan jami'an 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa taron zai maida hankali ne kan batutuwan da suka shafi babban zaɓen 2023 dake tafe da kuma cin mutuncin dakarun 'yan sanda a bakin aiki.
Sauran abubuwan da ake sa ran manyan jami'an zasu tattauna sun haɗa da bazaranar da hukumar ke fuskanta, taruka da wasannin jami'an yan sanda da dai sauran batutuwa masu muhimmanci.
Mataimakan Sufeta Janar na 'yan sandan ƙasa (DIGs), kananan mataimakan sufeta na ƙasa (AIGs) da kwamishinonin yan sanda daga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja na daga cikin mahalarta taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika, bayanai sun nuna cewa sauran waɗanda suka halarci taro da shugaban yan sandan sun haɗa da duk wasu manyan jami'ai a hukumar yan sanda daga sassan Najeriya.
Wannan taro na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake samun Kes ɗin hatsaniya tsakanin fararen hula da dakarun yan sanda sanye kaki kuma a bakin aiki.
A baya-bayan nan, an jiyo mai magana da yawun yan sanda na ƙasa, CSP Olumuyiwa Adejobi, yace bai kamata mutane su riƙa rama ko menene ɗan sanda ya musu ba matukar yana sanye da kayan aiki
Wasu nasarorin yan sanda a Zamfara
A wani labarin kuma Dakarun yan sanda sun samu gagarumar nasara a kokarin su na tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara
Yan sanda sun ce sun kama wani babban ɗan bindiga da ya addabi mutane, Umar Namaro, a jihar Zamfara.
Muhammed Shehu, kakakin yan sandan jihar yace dakaru sun kama wani Sojan Bogi ɗauke da muggan makamai a jihar.
Asali: Legit.ng