Shugaban CAC Ya Fadawa Kiristoci Wanda Ya Kamata Su Ba Kuri’arsu a Zaben Najeriya

Shugaban CAC Ya Fadawa Kiristoci Wanda Ya Kamata Su Ba Kuri’arsu a Zaben Najeriya

  • Samuel Oladele ya fadawa mabiyansa kiristoci cewa su tashi a gwabza da su a zaben da za ayi
  • Faston shi ne jagoran majami’ar Christ Apostolic Church (CAC) Worldwide mai mabiya a Najeriya
  • Kiran da Oladele ya yi a wajen wani taron addini da aka yi shi ne ayi la’akari da addini wajen zabe

Osun - Fasto Samuel Oladele wanda shi ne shugaban cocin Christ Apostolic Church (CAC) na Duniya ya ankarar da kiristoci a game da zabe mai zuwa.

Wani rahoto da Sun ta fitar a ranar Alhamis, ya nuna cewa Fasto Samuel Oladele ya halarci taron Fastoci na shekarar nan da cocinsa na CAC ya shirya.

A wajen wannan taro da aka yi a sansanin Ayo Babalola Memorial International Miracle da ke jihar Osun ne malamin addinin ya yi kira ga mabiyansa.

Kara karanta wannan

Jonathan: Abin Da Ya Sa Na Kira Buhari a Waya Kafin a Gama Kirga Kuri’un 2015

Samuel Oladele yake cewa zabe mai zuwa ba abin wasa ba ne, dole kiristoci su tashi tsaye wajen ganin sun kada kuri’a a kan abin da ya shafi lamarinsu.

Sai Kiristoci sun tashi-tsaye

“Dole ne mu maida hankali a kan zabe mai zuwa, ba za ta yiwu muyi wasa yayin da ake daukar matakan da suka shafi addininmu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za mu bi sharudan da kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta gindaya mana wajen zaben wanda zai zama sabon shugaban kasa a Najeriya.
'Yan takaran 2023
Manyan 'Yan takaran 2023 Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC
Ina mai fada da babban murya cewa sha’anin addini da lamarin Yesu ya fi komai muhimmanci."

- Samuel Oladele

PM News ta rahoto cewa an soki tikitin Musulmi da Musulmi na APC a taron bana mai taken: “Growing in the Grace and Knowledge of the Lord.”

Wanene na zaba a 2023?

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Fashe a Babban Birnin Jihar Arewacin Najeriya

Zaben shekara mai zuwa zai kasance ne tsakanin Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a karkashin APC, PDP, LP da NNPP.

Fasto Oladele ya zaburar da kiristoci cewa su duba addinsu kafin su zabi wanda suke ganin ya kamata zama shugaban kasa a babban zaben da za ayi.

A jawabinsa, faston bai kama sunan wani ‘dan takara ko jam’iyya ba, yace ana sa ran gobe za tayi kyau.

Rikicin PDP ya yamutse

Dazu muka samu labari tsohon Gwamnan Filato, Jonah Jang yace dama Nyesom Wike ake yaka a jam’iyyar PDP domin hana shi tikitin shugaban kasa.

Bayan an tsaida ‘dan takarar shugaban kasa, Jang yace shugaban PDP ya je gida yana taya Aminu Tambuwal murna, wannan ya nuna akwai makarkashiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel