Jam'iyyar PDP Ta Kira Zaman Gaggawa Bisa Ballewar Mabiya Wike

Jam'iyyar PDP Ta Kira Zaman Gaggawa Bisa Ballewar Mabiya Wike

  • Shugabannin jam'iyyar PDP sun fara ganawari sirri tun jiya kan neman mafita bayan ballewar mabiya Wike
  • Kakakin jam'iyyar PDP yace yau za'a cigaba da zaman kuma za'a yanke shawara kan lamarin
  • Rikicin jam'iyyar adawa ta PDP ta dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Atiku

Abuja - Uwar Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a ranar Laraba ta kira zaman gaggawa bisa baran-baran da wasu jiga-jiganta sukayi da yakin neman zaben jam'iyyar.

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da wasu jiga-jigan jam'iyyar sun sanar da cewa babu ruwansu da yakin neman zaben Atiku.

Sun lashi takobin cewa muddin Iyorchia Ayu zai cigaba da zama kan kujerar shugaba, babu ruwansu da jam'iyyar.

Sakamakon haka, shugabannin jam'iyyar sun shiga gannawar sirri don tattaunawa kan illar da hakan zai yiwa shirye-shiryen yakin neman zaben 2023.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

Wadata
Jam'iyyar PDP Ta Kira Zaman Gaggawa Bisa Ballewar Mabiya Wike
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta ruwaito Kakakin jam'iyyar, Debo Ologunaba da cewa sun fara zama ne tun lokacin da su Wike suke sanar da hannun riga da kamfen PDP.

A cewarsa, jam'iyyar za ta sanar da matsayarta kan hakan a yau (Alhamis).

Yace:

"A matsayinmu na jam'iyya, wajibi ne mu yi tsayin daka wajen sake gina jam'iyyarmu. Tun da safe (Laraba) muke zama. Abin farin cikin shine babu wanda ke adawa da dan takaran shugaban kasan mu."
"Zamu cigaba da zaman gobe (Alhamis) kuma daga baya mu sanar da matakin da zamu dauka."

Jerin Sunayen Gwamnoni, Tsaffin gwamnoni da, Ministoci Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku

Rikicin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Atiku.

Jiga-jigan wanda suka yiwa kansu lakabi magoya bayan Gwamnan jihar River, Nyesom Wike, sun hadu a daren Talata a gidansa inda suka yanke shawarar baran-baran da yakin neman zabe jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP 14 Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku, Gwamnoni, Tsaffin Ministoci, Iyayen Jam'iyya

Zaku tuna cewa Jam'iyyar PDP ta nada Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal matsyain Dirakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel