Rasha Ta Gwada Makami Mai Linzami Mafi Hadari a Duniya, zai Fara Aiki a 2026
- Kasar Rasha za ta fara amfani da sabon makamin Sarmat da aka bayyana shi a matsayin mafi ƙarfi a duniya a ƙarshen shekarar nan
- Bincike ya nuna cewa an ƙera makamin ne domin ɗaukar kananan makaman nukiliya zuwa wuraren da ke nesa da Rasha a fadin duniya
- A bayanin da ya yi, Vladimir Putin ya ce ƙarfin makaman da makamin ke ɗauke da su ya fi duk wani makamancinsa a kasashen Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Russia ta gwada wani sabon makami mai linzami mai ɗauke da makaman nukiliya mai iya kai hari daga nahiya zuwa nahiya.
Rahotanni sun nuna cewa Rasha ta yi makamin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinta na sabunta ƙarfin makaman nukiliyarta.

Source: Getty Images
Bayanin Putin kan makamin
Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa Vladimir Putin ya yaba da gwajin kwanaki kaɗan bayan ya bayyana cewa yaƙin Ukraine na gab da ƙarewa.
“Wannan shi ne makamin linzami mafi ƙarfi a duniya,”
In ji Putin game da makamin Sarmat a ranar Talata, yana mai cewa ƙarfin makaman nukiliyarsa masu iya kai hari wurare daban-daban ya fi na makamantansa na ƙasashen Yamma sau huɗu.
Putin ya ce makamin nukiliyar Sarmat zai fara aiki a ƙarshen shekarar nan. An ƙera shi ne domin maye gurbin tsohon makamin Voyevoda da aka gina a zamanin Tarayyar Soviet.
Mene ne Sarmat da Rasha ta yi?
RS-28 Sarmat, wanda ake kira “Satan II” a ƙasashen Yamma, wani makami ne mai iya kai hari daga nahiya zuwa nahiya — wato makamin ƙasa-da-ƙasa da aka ƙera domin isar da makaman nukiliya mai mafi ƙarancin zango na kilomita 5,500.
Putin ya ce makamin na iya isa wajen mai nisan fiye da kilomita 35,000 — wanda ya fi na makamantansa a ƙasashen Yamma nisa sosai kuma ya yi iƙirarin cewa zai iya:
“Tsallake duk tsarin kariyar makaman linzami na yanzu da wanda za a yi a gaba.”

Source: Getty Images
Sai dai masana a ƙasashen Yamma sun kiyasta cewa ainihin matsakaicin zangonsa na iya kasancewa kusan kilomita 18,000.
Reuters ta wallaffa bidiyon makamin a shafinta na X:
Yaushe aka fara kera makamin
Rahoto ya nuna cewa an fara aikin ƙera makamin tun 2011, kuma zai maye gurbin kusan makaman Voyevoda 40 da aka ƙera a zamanin tarayyar Soviet.
Bayan gwajin harba makamin a ranar Talata, Putin ya ce makamin Sarmat zai sa duk wani tsarin kariyar makaman Amurka ya zama marar amfani.
Turkiyya ta fitar da sabon makamin
A wani labarin kun ji cewa kasar Turkiyya ta yi taron baje kolin fasaha na 2026, inda ta bayyyana wani makami mai suna Yildirimhan.
Gwamnatin kasar Turkiyya ta sanar da cewa Yildirimhan na iya kaiwa nahiyoyin duniya kamar Afrika, Asia da Turai idan aka harba shi.
Wani rahoto ya nuna cewa kasar ta cigaba da shirin mallakar manyan makamai ne domin kare kanta daga dukkan baraza da zama mai tarisi a duniya.
Asali: Legit.ng

