Gada Ta Karye a Kaduna, Mutum 1 Ya Mutu, Gonaki Sun Wanke a Wata Ambaliyar Ruwa

Gada Ta Karye a Kaduna, Mutum 1 Ya Mutu, Gonaki Sun Wanke a Wata Ambaliyar Ruwa

  • Yayin da ruwan sama ke ci gaba da sauka, bangarori da dama a Najeriya na ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwan sama
  • Wata gada ta karye a jihar Kaduna, mutum daya ya rasu a lokacin da yake kokarin tsallaka ta a yankin Zaria
  • Ana kira ga gwamnatoci da su kawo dauki domin tabbatar da kare rayukan al'umma da ke rayuwa a yankin

Zaria, Kaduna - Biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ambaliyar ruwa ta karya gadar Maliki da ke Zaria a jihar Kaduna, mutum daya ya rasu yayin da ruwa ya wanke gonaki da dama.

Idan baku manta ba, yankuna da dama a Zaria sun fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a kwanakin baya, lamarin da ya kai ga rushewar gidaje da lalacewar gonaki, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hauhawar Farashin Kaya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

Yadda gada ta karye a Kaduna, mutum daya ya mutu
Gada Ta Karye a Kaduna, Mutum 1 Ya Mutu, Gonaki Sun Wanke a Wata Ambaliyar Ruwa | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Mutawakkilu Yusuf Rafin Yashi, Kakakin Yammacin Zazzau ya bayyana cewa, gadar Maliki-Kafin Mardan da ke hada al'ummomi sama da 20 da birnin Zaria ta rushe bayan mamakon ruwa a ranar Talata.

Ya kuma bayyana sunan mutumin da ya mutu da Alhaji Awwal Balarabe da yace ya rasu ne a hanyarsa ta dawowa daga kasuwa a Zaria.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutawakkilu ya kuma yi karin haske da cewa, mutumin ya taho ne da mota, sai ya ga ruwa ya mamaye gadar, daga nan ya ajiye motarsa domin ya tsalla cikin rashin sanin gadar ta karye gaba daya.

Yayin da ya kai ga kan gadar, ya fada ruwa ya nutse, lamarin da ya zama sanadiyyar rasa rayuwarsa.

Hakazalika, ya ce an gano gawar mamacin a ranar Laraba da safe, kuma an binne shi daidai da koyawar addinin Islama.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Matakin da ake dauka a yanzu

Ya zuwa yanzu, matasan yankin sun taru domin tabbatar da gyara gadar ta hanyar aikin gayya da suka fara.

Mutawakkilu ya kuma yi karin haske da cewa, aikin matasan yana da matukar tasiri wajen kare al'ummar yankin da dukiyoyinsu.

Ya kuma ce aikin matasan ana yin sane duk shekara, inda ya tuna da yadda a bara aka samar da motoci 20 na kasa da buhunnan siminti 20 da kudinsu ya kai N300,000 da al'ummar ta samar don gyara gadar.

Mutawakkilu ya kuma roki gwamnatin karamar hukuma da ta jiha da su gaggauta kawo dauki ga gadar domin samar da hanya mafi sauki wajen wucewa.

Mutanen Kauye da Ke Shirin Tserewa Harin ’Yan Bindiga Sun Nutse a Kogi a Abuja

A wani labarin, mutum biyar; maza hudu da wata matar aure sun nuste a garin tserewa harin 'yan bindiga a kauyen Chakumi a unguwar Gurdi ta Abaji a Abuja.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Ruwa: Mutum 92 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Gwamna Ya Lula Yawon Shakawata Ketare

Rahoton Daily Trust ya ce, Chakumi gari ne mai makwabtaka da kauyen Daku mai hade da kogin Gurara a unguwar Dobi ta Gwagwalada a birnin na Abuja.

Mai garin Chakumi, Mohammed Magaji ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce hakan ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Laraba 21 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel