Shugabannin Arewa Daga Jihohi 19 da Abuja Sun Fadi Wanda Zasu Mara Wa Baya a 2023

Shugabannin Arewa Daga Jihohi 19 da Abuja Sun Fadi Wanda Zasu Mara Wa Baya a 2023

  • Manyan Arewa sun yanke ɗan takarar shugaban ƙasar da zasu mara wa baya a babban zaɓen 2023 dake tafe
  • A wurin wani taro na kwana biyu da ya gudana a Abuja, Jagororin arewa sun ce dole sai wanda zai kawo karshen matsalolin yankinsu
  • Arewacin Najeriya na fama da matsalar tsaro wanda kusan ya mamaye mafi yawan jihohi har da Abuja

Abuja - Jagororin yankin arewacin Najeriya sun bayyana cewa zasu goyi bayan ɗan takarar shugaban kasa mai dabaru da kwarewar da zai kawo karshen matsalar tsaro da sauran matsalolin da suka addabi yankinsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa manyan arewan, daga jihohi 19 da birnin tarayya, sun bayyana haka ne a wurin taron kwana biyu da ƙungiyar Arewa New Agenda (ANA) ta shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Wani Azababben Yaƙi Ya Kaure Tsakanin Bello Turji da Tawagar Ƙasurgumin Ɗan Binidiga, Ɗan Bokolo

Manyan yan takara uku.
Shugabannin Arewa Daga Jihohi 19 da Abuja Sun Fadi Wanda Zasu Mara Wa Baya a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar shugabannin arewa, taɓarɓarewar tsaro, rashin haɗin kai, da koma baya da sauran matsaloli da suka kewaye yankin sun hana tare da daƙile haɓakar arewa.

Haka zalika sun koka bisa gazawar shugabanni wajen tsara kudirori da ɗaukar matakan lalubo hanyar warware tulin matsalolin da suka hana arewa motsa wa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakatare Janar na kungiyar kare muradun arewacin Najeriya (ACF), Murtala Aliyu, yace ya zama wajibi yankin, "Ya tashi tsaye ya ƙara ƙaimi da tattauna wa da jagororin siyasar ƙasar nan domin tabbatar da samun cigaba cikin hanzari."

Matsayar Sakataren ta samu goyon bayan Daraktan kula da gidan tarihi Arewa House, Dakta Shu'aibu Aliyu, wanda a jawabinsa, ya nuna cewa har yanzun arewa ce tushen haɗin kan ƙasar nan.

Sanata Ahmad Moallahyidi, wanda ya jagoranci shirya taron na kwana biyu, ya yi bayanin cewa bisa la'akari da faɗin ƙasa a arewa da ya kai hecta 98.2, wanda daga ciki ana iya noma hecka 82, yankin ya zarce cikin yan Najeriya kaɗai.

Kara karanta wannan

Tsohon SGF a Mulkin Buhari da Wani Jigon APC Sun Sha Alwashin Yakar Tinubu/Shettima a 2023

A cewarsa, adadin noman da za'a yi arewa zai iya gamsar da kafatanin nahiyar Afirka ta yamma, inda ya ƙara da cewa ya zama wajibi a magance matsalolin don cimma ga ci.

Tinubu Bacci zai rinka yi idan ya zama shugaban kasa - NNPP

A wani labarin kuma kun ji cewa Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufai Ahmed Alkali, ya yi gargadi cewa dan takarar APC, Bola Tinubu zai zama ‘shugaban kasa mai likimo’ idan aka zabe shi a 2023.

Alkali ya gargadi masu kada kuri’u da su tabbatar da ganin cewa basu zabi tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel