An Kashe Mutane 5,000 a Hare-Hare 200 Akan Al’ummar Benue Cikin Shekaru 11, Inji Ortom

An Kashe Mutane 5,000 a Hare-Hare 200 Akan Al’ummar Benue Cikin Shekaru 11, Inji Ortom

  • Gwamnan jihar Benue ya bayyana kadan daga yadda 'yan jiharsa suka fuskanci matsaloli na harin 'yan ta'adda
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Ortom ya ce akalla mutum 500 ne suka rasa rayukansu a Benue cikin shekaru 11
  • Najeriya na yawan fuskantat hare-hare da barnar 'yan ta'adda, musamman tun bayan barkewar Boko Haram a 2009

Jihar Benue - A hare-hare kusan 200 da aka kai jihar Benue, akalla mutane 5000 ne suka rasa rayukansu ta sanadiyyar barnar tsageru cikin shekaru 11, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Samuel Ortom ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 21 ga watan Satumba a yayin sanya hannu kan kudirin doka na zaman lafiya da sulhu na jihar tasa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shiga dajin Sambisa, sun sheke 'yan Boko Haram 36, sun ceto mutane da yawa

Gwamna Ortom ya ce jiharsa ta rasa mutane 5000 cikin shekaru 11
An Kashe Mutane 5,000 a Hare-Hare 200 Akan Al'ummar Benue Cikin Shekaru 11, Inji Ortom | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, wadannan tashe-tashen hankula da aka dinga samu sun yi sanadiyyar lalata hanyoyin samar da abinci a jihar.

A bangare guda, ya ce hakan ya haifar da yawan 'yan gudun hijira da kuma kawo koma-baya a fannin ilimi, lafiya da sauran hanyoyin ci gaba a Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ortom ya sha kokawa kan yadda ake samun rikice-rikice na kabilanci a jihar, inda yake yawan daura laifin kan Fulani makiyaya.

Rahoton majalisar dinkin duniya ta hannun kodinetan muhalli da ayyukan jin kai Matthias Schmale ya ce, akwai akalla kabilu sama da 374, harsuna 552 a tsakanin mutane sama da miliyan 206 a Najeriya.

Ya ce wannan albarka ce ga Najeriya, kuma babu abin da kasar za ta tunkara bata samu tare da wannan adadi mai yawa na al'adu ba.

Mutanen Kauye da Ke Shirin Tserewa Harin ’Yan Bindiga Sun Nutse a Kogi a Abuja

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai sabon hari Abuja, mutanen kauye sun nutse garin tserewa

A wani labarin, mutum biyar; maza hudu da wata matar aure sun nuste a garin tserewa harin 'yan bindiga a kauyen Chakumi a unguwar Gurdi ta Abaji a Abuja.

Rahoton Daily Trust ya ce, Chakumi gari ne mai makwabtaka da kauyen Daku mai hade da kogin Gurara a unguwar Dobi ta Gwagwalada a birnin na Abuja.

Mai garin Chakumi, Mohammed Magaji ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce hakan ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Laraba 21 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel