Dole a Zauna Lafiya: Bello Turji Da Wani Hatsabibin Dan Bindiga Sun Kaure da Yaƙi a Zamfara

Dole a Zauna Lafiya: Bello Turji Da Wani Hatsabibin Dan Bindiga Sun Kaure da Yaƙi a Zamfara

  • Wasu rahotanni sun nuna cewa tsagin Bello Turji ya kaure da azababben faɗa da ɓangaren wani shugaban 'yan ta'adda, Ɗan Bokolo
  • Wata majiya tace tawagar yan ta'addan biyu sun barke da yaƙi ne baya kai wasu hare-hare kauyuka a Shinkafi
  • A baya mataimakin gwamna Matawalle na Zamfara yace Turji ya tuba tare da alƙawarin taimaka wa gwamnati

Zamfara - Ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, da wani shugaban tawagar 'yan bindiga, Ɗan Bokolo, sun kaure da azababben yaƙi bayan kai hari kan bayin Allah a ƙauyukan Zamfara wanda ya lakume rayuka.

Wata majiya ta shaida wa jaridar Tribune cewa a baya-bayan nan, tawagar Ɗan Bokolo suka kai jerin muna nan hare-hare kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.

Babban ɗan ta'adda, Bello Turji.
Dole a Zauna Lafiya: Belli Turji Da Wani Hatsabibin Dan Bindiga Sun Kaure da Yaƙi a Zamfara Hoto: tribune
Asali: UGC

A cewar majiyar, waɗannan hare-hare sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, kana aka lalata garuruwa da ƙauyuka a yankin.

Yace wasu mutane suna zargin mayaƙan Bello Turji da kai harin, sai dai ya ƙara cewa da ƙyar Turji ya tsallake rijiya da baya a makon da ya gabata lokacin da jirgin soji ya saki bama-bamai a mafakarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fusata da waɗan nan muna nan hare-hare da aka kaiwa mutane, Turji ya yanke yaƙar tawagar Ɗan Bokolo da ƙarfin tsiya.

Bayanai sun nuna cewa mazauna yankunan Shinkafi da Moriki a yanzu sun fara barin ƙauyukan su biyo bayan yawan arangama tsakanin tawagar 'yan ta'addan biyu masu adawa da juna.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa hakan na zuwa ne bayan mataimakin gwamnan jihar ya sanar da cewa Turji ya tuba kuma ya yi alƙawarin taimaka wa gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

A makon da ya gabata, ance Sojoji sun ƙara zafafa kai samame sansanin Bello Turji bayan zargin yana da hannu a harin baya-bayan nan, wanda ya yi ajalin dakarun soji da dama.

Awanni 48 bayan samamen, rahoto ya tabbatar da cewa gomman yan fashin daji sun sheƙa barzahu a dazukan jihar Zamfara.

Wata majiya tace, "An shirya kai samamen ta sama da ƙasa a 'yan kwanaki masu zuwa a jihar Zamfara da wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya."

A wani labarin kuma kun ji cewa An Kama Sojan Bogi da Wani Ƙasurgumin Dan Bindiga a Jihar Zamfara

Yan sanda sun ce sun kama wani babban ɗan bindiga da ya addabi mutane, Umar Namaro, a jihar Zamfara.

Muhammed Shehu, kakakin yan sandan jihar yace dakaru sun kama wani Sojan Bogi ɗauke da muggan makamai a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel