Jerin Sunayen Gwamnoni, Tsaffin gwamnoni da, Ministoci Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku

Jerin Sunayen Gwamnoni, Tsaffin gwamnoni da, Ministoci Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku

Rikicin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Atiku.

Jiga-jigan wanda suka yiwa kansu lakabi magoya bayan Gwamnan jihar River, Nyesom Wike, sun hadu a daren Talata a gidansa inda suka yanke shawarar baran-baran da yakin neman zabe jam'iyyar PDP.

Zaku tuna cewa Jam'iyyar PDP ta nada Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal matsyain Dirakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa.

Hakazalika an nada Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, da sauran gwamnoni matsayin mambobin kwamitin.

Yanzu wasu mambobin kwamitin sun lashi takobin cewa lallai fa sai shugaban uwar jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya yi murabus za su yiwa jam'iyyar aiki a zaben 2023.

THISDAY ta ruwaito cewa wadanda suka halarci zaman sun hada da wasu gwamnoni, tsaffin gwamnoni, tsaffin ministoci, jiga-jigan jam'iyya, har da iyayaen jam'iyyar.

Atiku/Wike
Jerin Sunayen Gwamnoni, Tsaffin gwamnoni da, Ministoci Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku Hoto: AriseTV
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit ta tattaro muku sunayensu:

1. Tsohon mataimakin shugaban PDP, Cif Olabode George

2. Tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang

3. Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko

4. Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose

5. Tsohon gwamna jihar Cross River, Donald Duke

6. Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo

7. Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike

8. Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde

9. Tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana

10. Tsohon Ministan Shari'a, Aliyu Adoke

11. Mataimakin shugaban PDP na yankin kudu, Dan Orbih

12. Sanata Mao Ohabunwa

13. Dan takaran gwamnan PDP na jihar Nasarawa, Davematics Ombugadu

14. Hanarabul Nnenna

Anti Atiku
Jerin Sunayen Gwamnoni, Tsaffin gwamnoni da, Ministoci Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku
Asali: Facebook

Akwai Yiwuwar PDP Za Ta Sha Kaye A Zaben Shugaban Kasa Na 2023, In Ji Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ji

A baya, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Cif Bode George ya gargadi jam'iyyar hamayyar cewa za ta iya shan kaye a zaben 2023 saboda rikicinta, The Nation ta rahoto.

Ya ce yadda har yanzu aka gaza warware matsalar shugabanci a jam'iyyar zai iya shafan makomarsu a zaben 2023.

George, ya yi gargadin cewa PDP tana iya rabuwa biyu Jam'iyyar PDP ta Arewa da Jam'iyyar PDP ta Kudu, idan shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ki yin murabus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel