An Gano Makarantun Karya 349 Da Akayi Ikirarin Ana Ciyar Da Dalibai Abinci Kullum

An Gano Makarantun Karya 349 Da Akayi Ikirarin Ana Ciyar Da Dalibai Abinci Kullum

  • An bankado wasu makarantun da babu su a gaske, amma ana bada kudin ciyar da dalibai kulli yaumin
  • A cewar bincike, wasu jami'ai ke zuba kudin cikin aljihansu maimakon ciyar da daliban makarantun firamare a jihar Nasarawa
  • Kai tsaye an dakatar da jami'an ma'aikatar jin kai guda biyu kuma an nada wasu a madadinsu

A wani sabon magudi da aka bankado a aikin ma'aikatar jinkai da jin dadin al'umma, gwamnatin tarayya ta bankado makarantun karya 349 a jihar Nasarawa.

Kwamitin tattara bayanai na shirin ciyar da daliban makarantu na gwamnatin tarayya ce ta bankado wannan almundahanan.

Mallam Abdullahi Usman, wanda shine shugaban kwamitin kuma mai baiwa ministar jinkai Hajiya Sadiya Umar shawara ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai wajen gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

A cewarsa, wasu jami'an ma'aikatar ke cinye kudaden ciyar da dalibai a jihar.

Yace a farko, an shirya ciyar da makarantun gwamnati 1203 a fadin jihar.

Sadiya
An Magano Makarantun Karya 349 Da Akayi Ikirarin Ana Ciyar Da Dalibai Abinci Kullum
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Bayan bincike, kwamitin ta gano cewa makarantu 349 na karya ne babu su, yayinda wasu jami'ai ke zuba kudaden a aljihansu na ciyar da dalibai."

Ya kara da cewa wasu manya a ma'aikatar daga Abuja sun yi kira ga a cire jihar Nasarawa daga shirin gaba daya saboda wannan abinda ya faru.

Amma ba'a amince da hakan ba saboda 'yayan talaka ne zasu rasa.

Ya ce tuni an sallami shugaban shirin na jihar da jami'in da aka baiwa hakkin ayyukan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel