Yanzu Yanzu: Tubabbun Mayakan Boko Haram 20 Sun Mutu A Borno, An Bayyana Abun da Ya Kashe Su
- Annobar amai da gudawa ta barke a sansanin aikin hajji inda aka ajiye kimanin tubabbun yan ta’addan Boko Haram 12,000 a Maiduguri
- Rahotanni sun kawo cewa tubabbun mayakan Boko Haram 20 ne suka mutu sakamakon annobar yayin da wasu biyar suka mutu a sansanin yan gudun hijira
- Wata majiya a ma'aikatar lafiya ta ce mayakan kungiyar ta'addancin 11 ne suka mutu ba 20 ba
Borno - Daily Trust ta rahoto cewa akalla mutum fiye da 25 ciki harda tubabbun Boko Haram 20 ne suka mutu sakamakon barkewar annobar amai da gudawa a sansanin aikin hajji inda aka ajiye kimanin tubabbun yan ta’addan 12,000 a Maiduguri.
An tattaro cewa akalla mutum bakwai ne suka mutu a ranar Talata, 20 ga watan Satumba.
Rahoton ya kuma kawo cewa wasu mutum 14 sun mutu a sansanin aikin Hajji a ranar Laraba.
A cewar wata majiya, ma’aikatan jinya tare da goyon bayan kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya suna nan suna gwagwarmaya domin daidaita yawan mace-macen da ake samu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyar ta ce:
“Akalla tubabbun Boko Haram 20 ne suka mutu sakamakon barkewar annobar Kwalara a sansanin aikin Hajji sannan wasu hudu sun mutu a sansanin Bama, hakazalika, an rahoto cewa mutum uku sun mutu a sansanin Muna Garage.
Kimanin mutum 1,000 ne suka kamu zuwa yanzu, kuma daruruwa na karban magani a yanzu haka a cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban.”
Bugu da kari, wani babban ma’aikacin ma’aikatar lafiya wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da lamarin amma ya yi ikirarin cewa tubabbun Boko Haram 11 da wasu uku a sansanin yan gudun hijira na Muna Garage ne suka mutu sakamakon cutar, ba mutum 20 ba.
Majiyar ta ce ma’aikatar da abokan huldar ta na kan lamarin.
‘Yan Bindiga Sun Farmaki Coci, Sun Sace 40, Suna Neman Kudin Fansa N200m
A wani labari na daban, kungiyar mutanen kudancin Kaduna wato SOKAPU ta yi zargin cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mutum 40, harda yan coci a kwatas din Bayan Kasuwa da ke Kasuwan Magani, karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. Awemi Maisamari,ya gabatarwa manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, ya ce yan bindigar sun tuntubi yan uwan wadanda aka sace inda suke nemi a biya naira miliyan 200 kafin su sake su.
A cewar kungiyar, lamarin ya afku ne a ranar 12 da 13 ga watan Satumba, a yankin Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru, yan kilomita daga cikin birnin.
Asali: Legit.ng