Sarkin Argungu Ya Gabatar Da Wani Babban Bukata A Gaban Gwamnatin Birtaniya

Sarkin Argungu Ya Gabatar Da Wani Babban Bukata A Gaban Gwamnatin Birtaniya

  • Sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera, ya roki kasar Ingila da ta taimaka ta dawo masu da kayan tarihinsu
  • Basaraken ya bayyana cewa an daukewa masarautar Kabi wadannan kayayyakin ne a lokacin mulkin mallaka
  • Ya kuma mika ta'aziyyar babban rashi da gwamnatin Birtaniya tayi na mutuwar Sarauniya Elizabeth

Kebbi - Mai martaba sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera ya roki gwamnatin Birtaniya da ta taimaka ta dawo da wasu daga cikin kayayyakin tarihi na masarautar Kabi da aka tafi da su a lokacin mulkin mallaka.

Basaraken ya yi wannan rokon ne lokacin da ya karbi bakuncin babbar kwamishinar Birtaniya a Najeriya, Cantriona Laing a fadarsa da ke Argungu, jaridar The Nation ta rahoto.

Sarkin Argungu
Sarkin Argungu Ya Gabatar Da Wani Babban Bukata A Gaban Gwamnatin Birtaniya Hoto: Arewa Agenda
Asali: UGC

Sarkin ya yi bayanin cewa wasu daga cikin tsoffin kayan tarihin sun bata ne a lokacin mulkin mallaka a masarautar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina rokon gwamnatin Birtaniya da ta taimaka mana ta dawo da dukkanin kayan tarihinmu da suka bata zuwa masarautar Kabi."

Basaraken wanda ya samu wakilcin babban jigon masarautar Argungu, Alhaji Ibrahim Hassan, ya yiwa gwamnatin Birtaniya ta’aziyya kan mutuwar sarauniya Elizabeth.

Ya bayyana cewa tarihin Najeriya ba zai taba cika ba idan ba a ambaci rawar ganin da kasar Ingila ta taka ba.

Kwamishinar Birtaniyya, Catriona Laing, ta yaba da dan kwarya-kwaryan biki da aka yi mata da tawagarta a fadar sarkin.

Ta yi bayanin cewa Gwamna Atiku Bagudu ya fada mata abubuwa da dama game da jihar a bangaren al’ada, musamman bikin kamun kifi na Argungu, tarihin tattalin arziki da yadda jihar ta samu hadin kai da masarautu hudu.

Kwamishinar ta kuma ziyarci gidan kayan tarihi na Kanta da Rugar Fulani inda aka zagaya da ita don ganin al’adun mutanen.

Kara karanta wannan

Zamu Kara Albashin Ma'aikata Saboda Rayuwa Tayi Wahala: Chris Ngige

Ta kuma ziyarci kamfanin Wacot Rice Mill da ke Argungu inda ta zanta da mahukunta da ma’aikatan kamfanin, rahoton The Sun.

Tinubu Babban Kadarane, Gwamna Ganduje Ya Bayyana Kadan Daga Halayen Tinubu

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa idan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe zabe zai bunkasa kasar tare da kawo ci gaba.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake karbar nadin da aka yi masa a matsayin uban kungiyar ANIM a gidan gwamnati da ke Kano, Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel