Latest
A karo na biyu, dala ta sake tashi yayin da darajar naira ta zube inda ake siyar sa ita N1,234 a kasuwanni yayin bankin CBN ke kokarin shawo kan lamarin.
Tsohon Sarkin Damaturu na farko, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiyya ya na da shekaru 82 a duniya bayan fama da jinya.
Hukumar kididdiga ta ƙasa ta bayyana cewa matsakaicin farashin litar man fetur shi ne N630, mun haɗa masu jerin jihohin da fetur ya fi arha a watan Afrilu.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sanar da rage kuɗin da ɗalibai ke biya duk shekara a jami'ar jihar, ya kuma ƙarawa malamai da ma'aikata albashi.
Masu ruwa da tsakin APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya sun fara neman a dawo da kujerar shugaban jam'iyyar APC na kasa zuwa yankinsu, sun yarda a dakatar da Ganduje.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai sake yin tafiya ranar Talata zuwa ƙasar Hollan domin kai ziyarar aiki, daga nan zai wuce ya halarci taron WEF a ƙasar Saudiyya.
Wata mata mai shekaru 35 ta yanke jiki ta fadi, ta kuma mutu nan take a sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Benue. Ta mutu ta bar yara shida har da 'yan biyu
Rundunar sojin Najeriya ta gano wurin da 'yan ta'adan ISWAP ke hada burodi a jihar Borno. Sojojin sun lalata wurin tare da sauran kayan hada burodin
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ziyara ta musamman ga dakataccen sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi ranar Litinin.
Masu zafi
Samu kari