Bola Tinubu Zai Sake Ficewa Daga Najeriya Zuwa Wasu Ƙasashe 2, Bayanai Sun Fito

Bola Tinubu Zai Sake Ficewa Daga Najeriya Zuwa Wasu Ƙasashe 2, Bayanai Sun Fito

  • Bola Tinubu Tinubu zai bar gida Najeriya zuwa ƙasar Holland a wata ziyarar aiki da firaministan ƙasar ya gayyace shi
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce Tinubu zai gana da Sarki da Sarauniya, sannan zai wuce ya halarci taron WEF a Saudiyya
  • Ministoci da manyan jami'an gwamnati ne ake sa ran za su raka Tinubu zuwa waɗannan ƙasashe kuma zai bar Abuja gobe Talata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa ƙasar Netherlands ranar Talata, 23 ga watan Afrilu a wata ziyara ta aiki.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Atiku da jigon PDP sun gana da Sanatan Arewa da aka dakatar, bidiyo ya bayyana

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Bola Tinubu zai sake shillawa zuwa ƙasashen waje Hoto: Dolusegun
Asali: Facebook

Ngelale ya bayyana cewa Bola Tinubu zai kai wannan ziyara ne bayan Firaministan ƙasar Netherlands, Mark Rutte, ya aiko masa da goron gayyata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da Tinubu zai yi a Netherlands

Yayin da yake kasar Netherlands, Tinubu zai tattauna da firaministan ƙasar sannan kuma zai yi ganawa ta daban da Mai Martaba Sarki, Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima.

Sarauniyar ita ce mai ba da shawara ta musamman ga sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin kuɗi (UNSGSA).

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, D Olusegun ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na manhajar X.

"A Netherlands, Tinubu zai halarci taron kasuwanci da zuba jari na Najeriya da Holland wanda zai hada shugabannin kungiyoyi da ƴan kasuwar kasashen biyu da nufin lalubo damarmakin hadin gwiwa da aiki tare.
"Za a kuma yi tattaunawa mai zurfi tare da jami'an ƙasar kan ayyukan sarrafa tashar jiragen ruwa wanda suke da kwarewa kuma sun shahara a duniya."

Kara karanta wannan

JAMB: Gwamnatin Tinubu ta faɗi mafi ƙarancin shekarun shiga Jami'a a Najeriya

- Ajuri Ngelale.

Tinubu zai halarci taro a Saudiyya

Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ya halarci wani taro na musamman kan tattalin arzikin dunuya (WEF) wanda za a yi a ranakun 28 da 29 ga Afrilu a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

Mista Ngelale ya bayyana cewa Tinubu zai samu rakiyar wasu daga cikin ministoci da jami'an gwamnati a wannan tafiya.

Gwamnati za ta ɗauki matakin shiga jami'a

A wani rahoton Gwamnatin Bola Tinubu ta fara shirin aiwatar da shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun shiga jami'a a Najeriya

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce a yanzu za ka ga ɗalibai ƴan shekara 15 da 16 suna zana jarabawar JAMB wanda bai dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel