Abin Tashin Hankali: Wata Ƴar Gudun Hijira ta Yanke Jiki, Sai Dai Aka Ɗauki Gawarta

Abin Tashin Hankali: Wata Ƴar Gudun Hijira ta Yanke Jiki, Sai Dai Aka Ɗauki Gawarta

  • Mazaunan wani sansanin ƴan gudun hijira da ke jihar Benue sun shiga ruɗani bayan ɗaga cikinsu ya yanke jiki ta faɗi.
  • Hembadoon Tarhemba, ƴar gudun hijira mai yara shida ce wacce iftila'in ya afka mata kuma aka ɗauke ta ba rai
  • Marigayiyar ta bar yara shida, ciki har da ƴan biyu da su ke cikin matsananciyar yunwa da rashin lafiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Benue - An shiga ruɗani yayin da wata mata ƴar shekaru 35, Hembadoon Tarhemba ta yanke jiki ta fadi, tare da mutuwa nan take a sansanin ƴan gudun hijira da ke Abagena a jihar Binuwe. Marigayiyar mai yara shida ta mutu a sansanin da ta nemi mafaka bayan kashe mijinta da ƴan bindaga su ka yi, kamar yadda tsohuwar shugabar mata a sansanin Esther Oota ta tabbatarwa Leadership News.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya bayyana abin da ya hana a samu cikakken tsaro a Najeriya

Matar ta yanke jiki ta fadi
Matar mai shekaru 35 da ta yanke jiki wajen tattaro itace ta mutu ta bar yara 6 (An kawo hoton nan ne domin misali kawai) Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Yadda Hembadoon ta mutu

A bayanin Esther Oota, ta ce sun fita tattaro itacen girki da sanyin safiyar yau ne lokacin da lamarin ya afku. Ta ce marigayiyar na tsaka da faskara itacen domin komawa sansanin ta ɗorawa yaranta girki, sai ta yanke jiki ta fadi. A cewar tsohuwar shugabar matan, suna ganin Hembadoon ta faɗi su ka yi ƙoƙarin ɗaga ta, amma tuni rai ya yi halinsa. Yanzu haka ƴan biyun marigayiyar da sauran yaranta huɗu na sansanin, inda rahotanni su ka ce ƴan biyun Alia da Mimidoo na cikin mawuyacin hali, da yunwa da ma rashin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa Hembadoon na shayar da 'yan biyunta lokacin da ta rasu.

Direba ya rasu a bakin aiki

A wani rahoton, wani direban motar bas ya rasa ransa ya na cikin tuƙa mota maƙare da fasinjoji a a jihar Kwara zuwa harabar jami'ar Ilorin (UNIILORIN). Wani fasinja da ya yi namijin ƙoƙari ya ce shi ne ya tuƙa motar domin ceto sauran fasinjojin da ke bas ɗin ganin yadda kowa ya fada cikin firgici.

Mahukunta a jihar sun bayyana cewa mutuwar ta lokaci guda ta jefa su cikin dimuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel