An Shiga Jimami Yayin da Tsohon Sarki a Yobe Ya Rasu a Saudiyya a Shekaru 82

An Shiga Jimami Yayin da Tsohon Sarki a Yobe Ya Rasu a Saudiyya a Shekaru 82

  • An shiga jimami bayan rasuwar tsohon Sarkin Damaturu a jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya riga mu gidan gaskiya
  • Tsohon Sarkin a jihar Yobe ya rasu ne bayan ya sha fama da jinya a kasar Saudiyya ya na da shekaru 82 a duniya
  • Sakataren Hukumar Alhazai, Usman Mai Aliyu Biriri ya tabbatar da mutuwar tsohon Sarkin ga manema labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Saudiyya - Sarkin Damaturu a jihar Yobe na farko, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya riga mu gidan gaskiya a Saudiyya.

Marigayin ya rasu ne a kasar Saudiyya bayan ya sha fama da jinya ya na shekaru 82 a duniya.

Kara karanta wannan

Neja: An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun sake hallaka sojoji tare da sace Kyaftin

Tsohon Sarki a Yobe ya rasu a ƙasar Saudiyya
Sarkin Damaturu na farko, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya rasu a Saudiyya. Hoto: @Lminkaeel.
Asali: Twitter

Yaushe marigayin ya riƙe Sarkin Damaturu?

An nada marigayin a matsayin Sarkin Damaturu a watan Agustan 1993 kafin cire shi a mulkin soja a shekarar 1995.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya taɓa riƙe kwamishinan kudi a jihar Borno lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a 1984.

Daily Trust ta tattaro cewa Mai martaba Biriri ya rasu ya bar mata daya da yara da yawa a kasar Saudiya bayan fama da jinya.

Sanarwar rasuwar marigayin daga iyalansa

Sakataren Hukumar alhazai a jihar Yobe, Usman Mai Aliyu Biriri ya tabbatar da mutuwar marigayin.

"Tabbas ya rasu, a maganar da muke yi yanzu mu iyalansa muna ci gaba da karbar gaisuwa daga jama'a, zan yi magana da ku daga baya lokacin da ya dace."

- Usman Mai Aliyu Biriri

Usman yayin sanar da mutuwar, ya ce marigayin ya rasu ne a wani asibitin Saudiyya inda ta ce za a sanar da lokacin sallar jana'iza a masallacin Makkah.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarkin Zazzau ya amince na naɗin ɗansa babban muƙami a masarautar

Kafin rasuwarsa, Biriri ya rike mukamin kwamishinan tarayya a Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) na tsawon lokaci.

Babban Basarake a Ondo ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa an tafka babban rashi a jihar Ondo bayan rasuwar fitaccen basarake da ake kira Olojoda na Oda.

Marigayin mai suna Julius Omomo ya rasu ne ya na da shekaru 83 a duniya bayan ya sha fama da jinya.

Wani daga cikin iyalan basaraken, Ade Adelakun shi ya bayyana mutuwar Sarkin a yau Lahadi 14 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel