Atiku da Jigon PDP Sun Gana da Sanatan Arewa da Aka Dakatar, Bidiyo Ya Bayyana

Atiku da Jigon PDP Sun Gana da Sanatan Arewa da Aka Dakatar, Bidiyo Ya Bayyana

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar tare da Dino Melaye sun ziyarci dakataccen sanatan Bauchi ta Tsakiya
  • A bidiyon da ya bayyana, an ga Melaye yana shaguɓe ga majalisar dattawan Najeriya kan dakatar da Sanata Abdul Ningi
  • Hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, wanda ya wallafa bidiyon wannan ziyara, ya yabawa dakataccen sanatan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen sanata, Abdul Ningi a jihar Bauchi.

Atiku, ɗan takarar shugabn ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya kai wannan ziyara ne tare da tsohon sanata, Dino Melaye.

Atiku, Ningi da Dino Melaye.
Atiku da Jigon PDP Sun Gana da Sanatan Arewa da Aka Dakatar Hoto: Atiku Abubakar, Abdul Ningi, Sanator Dino Melaye
Asali: Twitter

Abdul-Rasheed, mai taimakawa Atiku kan harkokin midiya ya wallafa faifan bidiyon ganawar Atiku da Sanata Abdul Ningi ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu zai sake ficewa daga Najeriya zuwa wasu kasashe 2, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A faifan bidiyon, an ga Sanata Melaye ya ɗaga murna yana cewa "datakacce, dakatacce," a daidai lokacin da yake gaisawa da Abdul Ningi.

Meyasa Atiku ya gana da Ningi?

Yayin ganawa da Ningi, tsohon mataimakin shugaban kasar ya jaddada wajabcin yin gaskiya a kowane ɓangaren gwamnati idan har al'umma ake son a yi wa hidima.

Atiku ya kuma faɗawa Sanatan cewa suna tare da shi a wannan yaƙi da ya fara wanda ya jawo aka dakatar da shi a majalisar dattawa.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X da yammacin ranar Litinin, Atiku ya ce:

"Yayin ziyarar da na kai wa Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, na jaddada muhimmancin gaskiya idan har ana son cika muradun ƴan Najeriya da kuma kawo ci gaba.

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi dalilin zaftare farashin man dizal zuwa N1,000

"Na kuma tabbatarwa Sanata Ningi cewa ba shi kaɗai bane a wannan yaƙin wanda ya janyo aka dakatar da shi a majalisar dattawa."

Meyasa aka dakatar da Ningi?

Sanata Abdul Ningi ya shiga matsala ne bayan ya yi zargin an yi cushe kuɗi a kasafin kudin 2024 a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

Ya yi zargin cewa kasafin kuɗin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke kokaɗin aiwatarwa ya sha banban da kasafin da majalisar tarayya ta amince da shi.

Bisa haka ne majalisar dattawa da dakatar da Ningi na tsawon watanni bayan ta amince cewa ba zai iya kare kansa da kwararan hujjoji ba.

Ganduje ya shiga sabuwar matsala

A wani rahoton masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC sun fara juyawa Ganduje baya kan batun dakatar da shi a gundumarsa da ke jihar Kano.

Wannan na zuwa ne bayan wani tsagin APC a gundumar Ganduje sun sake fitowa sun tabbatar da dakatar da shi a karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel