Hukumar FCCPC Ta Rufe Kantin da Ya Hana ’Yan Najeriya Sayayya a Abuja

Hukumar FCCPC Ta Rufe Kantin da Ya Hana ’Yan Najeriya Sayayya a Abuja

  • Hukumar FCCPC ta gano wani babban kanti a birnin tarayya Abuja da aka hana 'yan Najeriya shiga domin su yi sayayya
  • Shugaban hukumar, Boladale Adeyinka, ce ta tabbatar da gaskiyar lamarin yayin da ta kai ziyarar ba-zata kantin ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu
  • An ruwaito cewa matar da ke kula da kantin ta gudu amma hukumar ta sanar da matakan da ta dauka tare bayan rufe kantin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Hukuma mai kare hakkin masu amfani da kayayyaki da abokan hulda ta kasa (FCCPC) ta rufe babban kantin 'yan kasar Sin da ke Abuja saboda nuna wariya.

An ruwaito cewa kantin ya na nuna wariya ga 'yan Najeriya ne ta hanyar rashin ba su damar sayayya.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sun yi zanga zangar rashin yadda da kama Yahaya Bello a kotun koli

FCCPC
Hukumar FCCPC ta ce kulle kantin ya biyo bayan nuna wariya ga 'yan Najeriya ne. Hoto: @fccpcnigeria
Asali: Twitter

Jami'an hukumar FCCPC sun yi dirar mikiya a kantin ne ranar Litinin, 22 ga wantan Afrilu tare da rufe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta ruwaito cewa lokacin da FCCPC suka isa kantin, sun yi tambayoyi ga ma'aikatan wurin kuma sun tabbatar da cewa shugabar kantin ta gudu.

Sun kara da cewa matar 'yar asalin ƙasar Sin, Cindy Lou ta gudu ne da misalin karfe 8.26 na safe. Daga nan ne sai hukumar ta kulle kantin ba tare da bata lokaci ba.

Yaushe kantin ya kirkiro dokar?

Legit ta gano cewa a ranar Lahadi da ta gabata ne kantin ya kirkiro sabuwar dokar daina sayar wa 'yan Najeriya kayayyaki.

Sabuwar dokar ta jawo cece-ku-ce tsakanin 'yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta

A cewar jaridar Vanguard, wannan ne ya jawo hankalin hukumar ta je kantin domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Kara karanta wannan

Kungiyar fafutukar kafa kasar Yarabawa ta ba shugaba Tinubu wa'adin ware su daga Najeriya

Matakin da gwamnati ta dauka

Lokacin da ta ke magana bayan rufe kantin, shugaban FCCPC, Boladale Adeyinka, ta ce dalilin zuwansu wurin shi ne su tabbatar da gaskiyar lamarin kuma sun tabbatar da hakan sai dai mai kantin ta gudu.

Saboda haka ta ce kantin zai cigaba da zama a kulle har sai lokacin da matar ta bayyana a gaban hukumar.

Dalilin tsige shugaban FCCPC

A wani rahoton kuma, kun ji cewa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce Babatunde Irukera ba ya iya aiwatar da aikinsa yadda ya kamata, shi ya sa aka tsige shi daga shugaban hukumar FCCPC

Shugaban kasar ya aikawa majalisar dattawa da wasikar dalilin tsige Irukera ne yayin da ya nemi amincewar majalisar wajen tabbatar da tsigewar ta sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel