Sojoji Sun Gano Gidan Burodin ’Yan Ta’addan ISWAP a Jihar Borno

Sojoji Sun Gano Gidan Burodin ’Yan Ta’addan ISWAP a Jihar Borno

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar ganowa tare da lalata gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno
  • Sojojin sun samu nasarar ne bayan shafe sama da mako guda suna fafatawa tare da ƴan ta'addan da ke boye a lungun
  • Yan ta'addan da suke boye a yankin su ake zargi da kai hare-hare a yankuna da dama tare da lalata wayoyin sadarwa a cikin dazuka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Dakarun sojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai sun gano wani wuri da 'yan ta'addan ISWAP ke kera burodi a jihar Borno.

Nigerian army
Sojoji sun gano inda 'Yan Boko Haram ke samun abinci a Borno Hoto: Nigerian Army
Asali: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da cewa an gano gidan burodin ne a wani lungu da ke Maisani, Timbuktu Triangle a karamar hukumar Dambuwa.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun halaka sojoji da dama a wani mummunan kwanton bauna

Yadda aka gano gidan abincin Boko Haram

A cewar jaridar the Cable, a ranar Lahadin da ta gabata wani mai fashin baki a kan harkar tsaro, Zagazola Makama, ya bada sanarwar cewa sojoji sun gano gidan burodin yayin da suka kai wani farmaki yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasu rahotanni kuma an samu cewa gano gidan burodin ya zo ne bayana kai farmaki da sojojin suka yi na tsawon sati a maboyar 'yan ta'addan.

A cewar jaridar Punch kuma, sojojin sun yi nasarar lalata kayayyaki da dama a wurin ciki har da wurin hada burodin da sauran kayan hada shi.

Munin aikin 'yan ta'addan Boko Haram

'Yan ta'addan dai su ake zargi da kai hare-hare masu muni a yankunan jihohin Borno da Yobe tare da lalata wayoyin sadarwa da suka hada jihohin.

Kara karanta wannan

Neja: An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun sake hallaka sojoji tare da sace Kyaftin

A cewar Makama, duk kuma da irin hatsarin da yankin ke da shi da irin shirin da 'yan ta'addar suka yi, sojojin sun samu nasar kutsawa da nasara a kan su.

An kashe 'yan Boko Haram a Borno

A wani rahoton kuma, kun ji cewa sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a kan mayakan Boko Haram yayin wani arangama da suka yi a yankin Mafa da ke jihar Borno

A yayin fafatawa tsakanin sojoji da Boko Haram, dakarun Operation Hadin Kai sun halaka mayakan kungiyar ta'addancin masu yawan gaske.

Asali: Legit.ng

Online view pixel