Osun: Ruɗani Yayin da 'First Lady' 2 Suka Bayyana Wajen Tarbar Remi Tinubu, an Samu Mafita

Osun: Ruɗani Yayin da 'First Lady' 2 Suka Bayyana Wajen Tarbar Remi Tinubu, an Samu Mafita

  • An shiga rudani bayan samun 'First Lady' guda biyu a jihar Osun yayin tarbar matar shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu
  • An gano wasu takardu da ke yawo inda suke tarbar Remi zuwa jihar daga ofisoshin dukkan matan gwamnan guda biyu
  • Daga bisani gwamnatin jihar ta fitar da sanarwa inda ta fayyace asalin 'First Lady' a jihar wacce za ta tarbi Remi Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - An ga hatsaniya a jihar Osun yayin da matan Gwamna Ademola Adeleke suke shirye-shiryen tarbar matar shugaban kasa, Remi Tinubu.

Matan guda biyu dukkansu sun buga takardun tarbar matar shugaban kasa, Bola Tinubu.

Gwamna ya yi martani bayan samun 'First Lady' 2 a Osun kan tarbar Remi Tinubu
Gwamna Ademola Adeleke ya magantu kan samun 'First Lady' 2 a Osun kan tarbar Remi Tinubu. Hoto: @AAdeleke_01.
Asali: Twitter

Musabbabin samun rudani a Osun

Kara karanta wannan

"Tinubu ya dara su", Jigon APC ya fadi yadda Najeriya za ta kasance a hannun Atiku da Obi

Hakan ya biyo bayan kokarin tarbar Remi Tinubu da matan biyu Titilola Adeleke da Ngozi Adeleke suka yi, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran matar shugaban kasar za ta ziyarci birnin Osogbo na jihar a yau Talata 23 ga watan Afrilu.

Sai dai Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa Titilola ce za ta tarbi Remi Tinubu a matsayinta na uwargidar jihar.

Martanin Gwamnan Osun kan lamarin

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Olawale Rasheed ya fitar a jiya Litinin 22 ga watan Afrilu.

Rasheed ya ce babu wani cece-kuce kan matsayar ofishin uwargidar gwamna a jihar kamar yadda ake yadawa, a cewar Daily Trust.

Ya ce Titilola ita ce uwargida kuma ita ce za ta karbi bakwancin matar shugaban kasa a yau Talata 23 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

"Musulmi ne ko Kirista": APC da PDP sun gwabza kan ainihin addinin gwamna, an kawo hujjoji

Olawale ya ce sanarwar da aka fitar a baya ba daga ofishin Ngozi Adeleke ya fito ba, inda ya ce an cafke wanda ya haɗa rigimar kuma ya na shan tambayoyi.

APC ta kalubanci Gwamna Adeleke kan addininsa

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Osun ta kalubalanci Gwamna Ademola Adeleke kan ainihin addinin da ya ke bi guda daya.

Jam'iyyar ta bayyana haka ne yayin da gwamnan ke ayyana kansa a matsayin Musulmi kuma Kirista a lokaci guda.

A martaninta, jam'iyyar PDP ta ce APC ba ta da manufa shiyasa ta fake da maganar addini domin kawo rudani a jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel