Surukai, 'Ya 'yan Abokan Siyasa da Na Hannun Dama 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai a Mulki

Surukai, 'Ya 'yan Abokan Siyasa da Na Hannun Dama 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai a Mulki

Abuja - Wasu sun fara nuna damuwa game da yadda Bola Ahmed Tinubu yake gudanar da mulki musamman wajen nadin mukamai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ba a shekara guda da rantsar da shi ba, amma an fara jifan Bola Ahmed Tinubu da zargin fifita na kusa da shi idan aka tashi rabon kujeru.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Wani rahoto da Daily Trust ta fitar a ranar Asabar ya nuna yadda shugaban kasa ya zagaye kan shi da ‘yanuwa ko dai ‘ya ‘yan abokansa.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya ba mutanen na kusa da shi mukamai Hoto: @nosasemota
Asali: Twitter

Jerin na kusa da Tinubu masu mukamai

1. Oyetunde Ojo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanakin baya aka ji shugaban Najeriyan ya nada Oyetunde Ojo ya zama sabon shugaban hukumar kula da gidaje ta tarayya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace malamin addini a kokarin zuwa binne mahaifiyarsa, sun sace wasu 15

Abin da ya ja surutu shi ne Oyetunde Ojo mijin ‘yar shugaban kasar, Folashade Tinubu Ojo ce.

2. Temitope Ilori

Bola Tinubu bai manta da amininsa watau Bisi Akande ba, ya nada ‘diyarsa mai suna Temitope Ilori a matsayin shugaban hukumar NACA.

3. Umar Abdullahi Ganduje

Da aka tashi nada Darektoci a REA mai raba wutar lantarki a kauyuka, Umar Ganduje wanda mahaifinsa ke rike da APC ya samu gurbin Darekta.

4. Olufemi Akinyelure

Shugaban sashen bincike a aikin samar da wutar lantarki a Najeriya shi ne Olufemi Akinyelure wanda mahaifinsa ya samu mukami a NNPCL.

5. Muhammad Abu Ibrahim

Tun ba yau ba Sanata Abu Ibrahim yake tare da Tinubu, yana hawa mulki aka ji Muhammad Abu Ibrahim ya zama shugaban NADF.

‘Yan APC sun gamsu da kamun Tinubu?

Rahoto ya zo cewa wasu ‘ya ‘yan jam’iyya ba su jin dadin irin abubuwan da ke faruwa a gwamnati, an fara surutai a kan irinsu Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

An kawo misalin Dr Dakorinama Alabo George da aka ba rikon hukumar BCDA bayan an yi tunani daga Kebbi za a dauko sabon shugaban ta.

An yi wa Muhammadu Buhari wannan zargi, amma fadar shugaban kasa ta musanya batun, ta ce akwai wasu mukamai da za a raba.

Shugaba Tinubu ya cika 72

A jiya Bola Tinubu yake cika shekara 72 a duniya, ana da labari Muhammadu Buhari ya fitar da jawabin taya murnar kara shekara a ban kasa.

Godswill Akpabio ya ce Bola Tinubu shugaba ne mai hangen nesa da ke kawo sauyi a mulki, sauran ‘yan siyasa sun cigaba da kwararo yabo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel