Jerin Manyan Jihohi 10 da Farashin Litar Man Fetur Ya Fi Arha a Najeriya

Jerin Manyan Jihohi 10 da Farashin Litar Man Fetur Ya Fi Arha a Najeriya

  • Farashin man fetur na ɗaya daga cikin abubuwan da suka damu ƴan Najeriya bayan cire tallafin da aka yi a watan Mayu, 2023
  • A ƴan kwanakin nan, fetur ya ƙara arha a wasu jihohi sakamakon tashin Naira a kasuwar canji wanda ya sa abubuwa suka fara sauƙi
  • Legit Hausa ta tattaro maku jihohi 10 da farashin fetur ya fi arha kamar yadda rahoton hukumar kididdiga ta ƙasa ya tabbatar a watan Afrilu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin farashin litar man fetur a halin da ake ciki yanzu a Najeriya shi ne N630 zuwa sama.

Sai dai rahoton NBS ya gano cewa man fetur ya fi arha a yammacin ƙasar nan yayin da ƴan Arewa ke sayen kowace lita a farashi mafi tsada, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

JAMB: Gwamnatin Tinubu ta faɗi mafi ƙarancin shekarun shiga Jami'a a Najeriya

Gidan mai.
Yadda farashin man fetur ke da arha a wasu jihohi 10 a Najeriya Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro muku jihohin da suka fi arhar man fetur a halin yanzu, waɗanda mafi yawan jihohin na shiyyar Kudu maso Yamma ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin jihohin da farashin fetur

A nan kasa, mun lissafo maku jerin jihohi 10 da suka fi arha a farashin fetur kan kowace lita a watan Afrilu, 2024:

1. Jihar Legas - N630.75

2. Jigar Oyo - N645.88

3. Jihar Ogun - N651.25

4. Jihar Neja - N657.15

5. Jihar Ekiti - N661.56

6. Jihar Filato - N662.27

7. Jihar Ondo - N663.85

8. Jihar Kwara - N665.68

9. Jihar Osun - N672.14

10. Jihar Kaduna - N683.93

Farashin fetur a gidajen mai

Idan ba ku manta ba, a makon da ya gabata, mun kawo maku rahoton yadda farashin man fetur ya sauka a jihar Legas da ke Kudu maso Yamma

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka Farfesa tare da sace mutum 2 a wani sabon hari

A binciken da muka yi, litar man fetur ta ragu daga N650 zuwa N620 a wasu gidajen mai daban-daban a jihar.

Manajan ɗaya daga cikin gidajen mai ya shaida mana cewa sun samu sauki ne a sabon kayan da suka siyo shiyasa suka rage farashin zuwa N620.

Amma lamarin ya sha banban da abin da ke faruwa a jihar Katsina, inda wakilin mu ya ziyarci wasu gidajen mai kuma ya gano cewa litar Fetur ta kara tsada.

Shinkafa ta sauka a Kwara

A wani rahoton na daban yayin da 'yan Najeriya ke kuka tsadar rayuwa, a hankali farashin kayayyaki musamman na abinci na karyewa a kasar nan.

Na baya bayan nan shi ne karyewar farashin buhun shinkafa a jihar Kwara, inda a yanzu ake sayar da buhu mai kilo 50 kan N52,000 zuwa N54,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel