An Ɗauke Wuta a Jihohin Arewa 3 Yayin da Tsageru Suka Lalata Wayoyin Lantarki

An Ɗauke Wuta a Jihohin Arewa 3 Yayin da Tsageru Suka Lalata Wayoyin Lantarki

  • Kamfanin raba wuta TCN ya tabbatar da ɗauke wuta a wasu sassan Gombe, Adamawa da Taraba saboda katsewar wayoyin lantarki
  • A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Litinin, ya ce hasumiyoyi hudu da ke ɗauke da wayoyin raba wuta ne aka lalata a titin Jos- Gombe
  • Sai dai TCN ya tabbatar da cewa tuni injiniyoyi suka gano asalin matsalar kuma za su yi duk mai yiwuwa wajen gyarawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da faɗuwar wasu hasumiyoyin da ke ɗauke da wayoyin wutar lanyar a hanyar Jos-Gombe.

Kamfanin TCN ya bayyana cewa wasu ɓarayi sun lalata hasumiyoyin wuta guda huɗu a kan titin, wanda ya yi sanadin ɗauke wutar lantarki a jihohin Adamawa, Gombe da Taraba.

Kara karanta wannan

TCN: Ana kokarin gyara wutar lantarki bayan jihohi 3 sun shiga cikin Duhu

Wayoyin wutar lantarki.
An shiga duhu saboda rashin wutar lantarki a wasu sassan jihohi 3 Hoto: TCN
Asali: Facebook

TCN ya ce an katse wayoyin lantarki

Manajan sashin yaɗa labarai na kamfanin TCN, Ndidi Mbah ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin da daddare, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mbah y ce hasumiyoyin wutar lantarkin sun faɗi ne da misalin ƙarfe 3:32 na yammacin ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, jaridar Leadership ta tattaro.

Sakamakon haka wutar lantarki ta daina zuwa tashoshin rarraba wuta da ke Gombe, Yola da Jalingo, wanda ya sa aka ɗauke wuta a sassan jihohin.

Kamfanin TCN ya ɗauki matakin gyara

"Kamfanin TCN na tabbatar da cewa an lalata wasu hasumiyoyin wutar lantarki huɗu a hanyar Jos zuwa Gombe da misalin ƙarfe 3:32 na yammacin ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu.
"Bayan lura da cewa wayoyin da ke kai wuta mai nauyin 330kV sun lalace, jami'an kamfanin TCN sun yi ƙoƙarin gyarawa amma abun ya gagara.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno

"Yayin bin diddigin gano matsalar, injiniyoyin TCN sun gano cewa an lalata hasumiya mai lamba 288, 289, 290, da 291 kuma an sace wasu kayayyakinsu. Sannan sun faɗi ƙasa sakamakon lamarin.
"Za mu yi duk mai yiwuwa don maido da wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa yayin da ake kokarin sake gina wasu layukan wutar da aka lalata.”

- Ndidi Mbah.

Tinubu sai sake fita Najeriya

A wani rahoton Bola Tinubu zai bar gida Najeriya zuwa ƙasar Holland a wata ziyarar aiki da firaministan ƙasar ya gayyace shi.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce Tinubu zai gana da Sarki da Sarauniya, sannan zai wuce ya halarci taron WEF a Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel