Yayin da CBN Ke Kokarin Kawo Gyara, Naira Ta Samu Matsala a Karo Na 2, Dala Ta Tashi

Yayin da CBN Ke Kokarin Kawo Gyara, Naira Ta Samu Matsala a Karo Na 2, Dala Ta Tashi

  • Kwanaki kadan bayan sanar da faduwar darajar naira, a jiya Litinin 22 ga watan Afrilu ta sake cin karo da matsala
  • Naira ta sake faduwa akalla da kaso 5.5% idan aka kwatanta da ranar Juma'a 19 ga watan Afrilun wannan shekara
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnan bankin CBN, Yemi Cardoso ya yi alkawarin inganta darajar naira domin samun daidaito

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - A karo na biyu cikin 'yan kwanaki, Naira ta sake faduwa a kasuwanni yayin da dalar Amurka ta tashi.

Darajar naira ta fadi da kaso 5.5% idan aka kwatanta da farashin N1,169 kan dala a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

Duk da kokarin CBN kan daidaita naira, dala ta sake tashi a kasuwa
Dala ta sake tashi yayin da naira ta fadi a kasuwa duk da kokarin Babban Bankin Najeriya, CBN. Hoto: Central Bank of Nigeria, CBN.
Asali: UGC

Nawa ake saida Naira-dala a kasuwa?

Tribune ta tattaro cewa a yanzu ana siyar da dala kan farashin N1,234 a kasuwanni idan aka kwatanta da kwanakin baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan sake faduwar naira a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu da kaso 1.3% a kasuwanni.

Yemi Cardoso ya bayyana haka ne a ranar Asabar 20 ga watan Afrilu kwana daya bayan naira ta sake faduwa.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso ya ce suna bakin kokarinsu dokin inganta naira a kasaaar.

Cardoso ya bayyana haka ne a ranar Asabar 20 ga watan (CBN), Yemi Cardoso ya ce suna bakin kokarinsu dokin inganta naira a kasa, cewar Punch.

Matakan da CBN ke dauka kan Naira

Gwamnan CBN ya ce bankin ya na aiki tukuru domin tabbatar da farashin Naira ya inganta yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

“Magana ta gaskiya za a samu hawa da saukar farashi da kuma koma baya amma ko a jiya kun ruwaito yadda naira ta fara farfadowa a cikin dare."

- Yemi Cardoso

Dala ta sake tashi a kasuwa

A wani labarin mai kama da wannan, Naira ta sake faduwa a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu a kasuwannin 'yan canji.

A ranar kuma 19 ga watan Afrilu ana siyar da dala kan N1,169 a kasuwanni idan aka kwatanta da ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu kan N1,154.

Hukumar kula da cinikayyar kudi ta NAFEM ta tabbatar da cewa naira ta fadi da kaso 1.38% a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel