Latest
Kungiyar SERAP ta bawa shugaba Tinubu sa'o'i 48 kan janye harajin tsaron yanar gizo da za ta rika cirewa lokacin huldar kudi da bankuna ko ta maka shi a kotu.
Sanata Shehu Sani ya yi shaguɓe ga 'yan Najeriya bayan bankin CBN ya kakaba musu sabon haraji yayin da suke damuwa Bola Tinubu bai dawo daga taron Saudiyya ba.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun aikata sabon ta'addanci a jihar Zamfara bayan sum hallaka mutum takwas tare da sace manajan banki a wasu hare-hare.
Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta umurci majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan madafun iko ba tare da ɓata lokaci ba.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar da suka yi garkuwa da mutane 13 bayan harin da suka kai kauyen Piko, babban birnin tarayya Abuja sun nemi N900m kudin fansa.
Shugaban karamar hukumar Ikere-Ekiti, Olu Adamolekun ya rantsar da hadimansa da Alkur'ani da kuma gunki inda ya bukace su da su yi biyayya ga jam'iyyar APC.
Wasu ƴan fashin teku sun tare jirgin ruwa mai ɗauke da mutum 20 a kogin Onne ranar Litinin, sun yi masu tatas kana suka yi awon gaba da mutum bakwai ranar Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'adda sun kai wani harin ta'addanci a jihar Kaduna inda suka hallaka mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum 18.
Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta ja kunnen masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, inji Shugaban hukumar, Ola Olukoyede.
Masu zafi
Samu kari