Jam'iyyar APC Ta Fusata, Ta Umurci Majalisar Dokoki Ta Tsige Gwamna Nan Take

Jam'iyyar APC Ta Fusata, Ta Umurci Majalisar Dokoki Ta Tsige Gwamna Nan Take

  • Jam'iyyar APC ta buƙaci majalisar dokokin jihar Ribas ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan mulki nan take
  • APC ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan kalaman da Fubara ya yi kan sulhun da Bola Tinubu ya masu a rikicin siyasar Ribas
  • Gwamnan dai ya ce sulhun da aka yi ba ya cikin kundin tsarin mulki, inda ya ƙara da cewa doka ba ta san da zaman majalisar dokokin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ribas ta umurci majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

APC, wadda ke da mafi rinjaye a majalisar, ta umarci mambobin ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule su fara bin matakan doka na tsige Gwamna Simi Fubara nan take.

Kara karanta wannan

"Ban san da zamanku ba", Fubara ya yi kakkausar suka ga 'yan majalisar Rivers

Gwamna Fubara na jihar Ribas.
Jam'iyyar APC ta fusata da kalaman Gwamna Fubara kan sulhun rikicin siyasar jihar Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin riƙon kwarya na jam'iyyar APC, Tony Okocha ne ya sanar da haka a Fatakwal, babban birnin jihar ranar Talata, 7 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa APC ke son tsige Gwamna Fubara?

Jam'iyyar APC ta yi kira da a tsige Fubara ne biyo bayan kalaman da ya yi kan sulhun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi a rikicin siyasar jihar, cewar The Nation.

Idam za ku iya tunawa, shugaba Tinubu ne ya jagoranci yayyafawa wutar rikicin ruwan sanyi a wani taro da ya kira a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Amma a ƙarshen makon nan, Gwamna Fubara ya bayyana cewa wannan sulhun ba doka ba ce, sulhu ne na siyasa domin kawai a zauna lafiya.

Gwamna Fubara ya kuma ƙara da cewa idan da ya so da tuni ya rushen majalisar dokokin jihar domin doka ba ta san da zamansu ba.

Kara karanta wannan

"Da yawa ba su da muƙamai": Jigon APC ya magantu kan zargin rikicin Tinubu da El-Rufai

Wane laifi Gwamna Fubara ya aikata?

Da yake hira da manema labarai, shugaban APC na Ribas ya ce gwamnan ya aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi, don haka akwai bukatar a fara shirin tsige shi.

A rahoton Daily Trust, Okocha ya ce:

"Mun umurci ’yan majalisar dokokin jihar Ribas da su fara shirin tsige wannan gwamnatin ta masu farfaɗiya, wuyan gwamna ya riƙa, ya daina mutunta doka.
"Abin da yake so kaɗai yake yi, ba zamu tsaya mu zuba ido a matsayin ƴan asalin jihar Ribas muna gani jihar mu ta zama abin barkwanci ba."

Gwamnan Kano zai koma APC?

A wani rahoton na daban, Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya amince zai sauya sheƙa zuwa APC tun kafin hukuncin kotun koli.

Ya ce a halin yanzun gwamnan da tawagarsa sun bukaci ƙarin lokaci domin su kammala shirye-shiryen dawowa jam'iyya mai mulkin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel